Gwamnatin Tarayya ta bai wa Rahama Sadau muƙami

Rahama Sadau ta mika godiya ga Mataimakin Shugaban Kasa da ya ba ta wannan mukami.

Gwamnatin Tarayya ta bai wa Rahama Sadau muƙami

Rahama Sadau

Gwamnatin Tarayya ta naɗa fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau a matsayin mamba a kwamitin kula da shirin zuba hannun jari a fannin kirkire-kirkiren zamani (iDICE).

Jarumar ce ta bayyana hakan a Yammacin wannan Alhamis ɗin cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook.

A cikin saƙon, Rahama Sadau ta miƙa godiya ga Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima da ya ba ta wannan muƙami bisa la’akari da cancantarta.

Bayanai sun ce a Larabar da ta gabata ce mataimakin shugaban kasar ya ƙaddamar da kwamitin shirin iDICE wanda ke da alhakin lalubowa tare da tallafa wa mutane ko wasu kamfanoni da suke da wata fikira ta zamani musamman a ɓangaren tsare-tsare da dabaru a fannin sana’o’i.

Rahama Sadau ta kuma bayyana cewa Shirin iDICE haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da hukumomin duniya da suka haɗa da Bankin Masana’antu, Bankin Bunkasa Afirka, Hukumar Bunkasa Faransa, da kuma Bankin Bunkasa Musulunci.

Wasu hotuna da jarumar ta wallafa dangane da sabon mukamin da ta samu: