Gwamnatin Tarayya ta bai wa ’yan Kasuwar Singa tallafin Naira biliyan biyar

Kashim Shettima ya kuma garzaya filin wasa na Sani Abacha domin halartar taron karɓar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.

Gwamnatin Tarayya ta bai wa ’yan Kasuwar Singa tallafin Naira biliyan biyar

Gwamnatin Tarayya ta sanar da bayar da tallafin naira biliyan 5 ga waɗanda ibtila’in gobara ya shafa a Kasuwar Singa da ke Jihar Kano.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a yayin wata ziyarar jaje da ya kai kasuwar a ranar Litinin.

Da yake jawabi, Shettima ya bayyana gobarar a matsayin babbar masifa ga ƙasa baki ɗaya, ba Kano kaɗai ba, inda ya yi addu’ar Allah Ya kiyaye aukuwar irin wannan iftila’i a gaba.

Aminiya ta ruwaito cewa, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya samu rakiyar gwamnonin jihohin Jigawa, Kebbi da Imo.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Singa, Junaid Zakari, ya yaba da tallafin da Gwamnatin Tarayyar ta bayar.

Ya jaddada cewa za a yi amfani da kuɗin yadda ya dace domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuma farfaɗo da harkokin kasuwanci.

Ana iya tuna cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce gobara ta tashi a Kasuwar Singa wadda ta riƙa ci har zuwa wayewar gari Lahadi, inda ta ƙone sama da shaguna da rumfuna 1,000 a ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a Nijeriya.

Hukumar kashe gobara ta ce har yanzu ana bincike domin gano musabbabin gobarar da girman asarar da aka yi.

Bayan ziyarar, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma garzaya filin wasa na Sani Abacha da ke Kofar Mata domin halartar taron karɓar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.