Tinubu ya bayar da umarnin sayar wa Dangote ɗanyen mai
Gwamnatin ta ce za ake sayar da ɗanyen man ne a farashin Naira.
Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin fara sayarwa da matatar Dangote da sauran matatun mai masu buƙatar ɗanyen mai.
Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa (FEC) na gaggawa da aka gudanar a ranar Litinin.
Majalisar ta kuma bayar da umarnin sayarwa da masu buƙata ɗanyen mai a Naira a maimakon Dala.
Da yake yi wa manema labarai ƙarin haske, shugaban hukumar tattara haraji na ƙasa, Zacch Adedeji ya ce wannan zai sauƙaƙawa masu sayen ɗanyen mai a cikin gida.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce daga yanzu gwamnati ta soke duk wani cinikin ɗanyen mai a cikin gida da Dala.
Bayanai na nuna cewa matatar mai ta Dangote kaɗai na buƙatar manyan jiragen ruwa 15 na ɗanyen mai a kowace shekara, inda jimillar kuɗinsu ya kai Dala biliyan 13.5.
Sai dai kamfanin mai na ƙasa (NNPC), ya ce zai iya samar da guda huɗu ne kacal.
Majalisar zartaswar a yayin zamanta na yau ta amince da bai wa matatar mai ta Dangote da sauran ƙananan matatu da ke cikin gida ganga 450,000 a kowace rana, kuma za a riƙa lisaffin ne a Naira kan canjin Dala na kowace rana.