Gwamnatin Tarayya ta bukaci manoma su rika noman da zai kewaye shekara

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce akwai bukatar manoma su kara yin tsayin daka wajen bunkasa nomansu ya rika kewaye shekara; tana mai cewa yanzu an wuce noman yanayi guda. Inda ta ce hakan zai sa tattalin arzikin kasar bangaren noma ya tsayu da kafafunsa. Manajan Darakta a Hukumar Kula da Ci gaban Karamin Gulbin Neja […]

Gwamnatin Tarayya ta bukaci manoma su rika noman da zai kewaye shekara

Wata gonar shinkafa a yankin Bula a Jihar Bauchi

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce akwai bukatar manoma su kara yin tsayin daka wajen bunkasa nomansu ya rika kewaye shekara; tana mai cewa yanzu an wuce noman yanayi guda. Inda ta ce hakan zai sa tattalin arzikin kasar bangaren noma ya tsayu da kafafunsa.

Manajan Darakta a Hukumar Kula da Ci gaban Karamin Gulbin Neja da ke karkashin Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta Tarayya, Injiniya Adeniyi Saheed Aremu ya fadi haka a wurin bayar da horo na kwana hudu kan koyo da fadada aikin  amfani da ruwa ga masu ruwa da tsaki da masu amfani da ruwan, wanda ya gudana a birnin Ilorin na Jihar Kwara.

“Ba mu bukatar manoman yanayi guda, sai dai manomin da zai kewaye shekara yana noma. Abin da ka sani ne abinci abin da ake nema ne kullum. Shekaru da dama da suka wuce muna bukatar abinci. Yau ma haka muna bukatarsa a lokaci mai zuwa ma haka muna bukatar abinci, za mu ci gaba da bukatar abinci gashi al’ummarmu na kara yawa,” a cewarsa.

Ya yi tsokaci kan rufe iyakokin kasar da aka yi, inda ya ce karin farashin shinkafar gida da aka samu a yanzu ya faru ne sakamakon yawan bukatarta da ake yi. Muna bukatar fadada hanyoyin nomanta.”

Dakta Aremu ya ce bayar da horo zai taimaka wajen fadada aikin koyar da manoma yanda za su yi amfani da ruwa ga  sanin abin da shukarsu ke bukata da sauran abubuwa, hakan zai sanya su yi matukar amfana da albarkar kasar da gulbin.

Dakta Ahmed A. Zik-Rullahi Babban Jami’i a Kamfanin Amzik masani ne a haujin  ya ce shirin a dunkule ya fito da yadda tattalin arzikin Najeriya ke girma ta bangaren girma da ci gaba a fannin noma da amfani da albarkatun ruwa a zamanan ce.

Ya ce horon zai karfafa girman fadada ayyuka ga mutum daya da kuma  dukkan masu ruwa da tsaki da ke kula da ruwa a harkar noman rani da kiwon kifi, kula da wuraren noma, tsaron gona, magance hasara, rigimar manoma da kuma dangantaka tsakanin manoma da kamfanoni.