Gwamnatin Tarayya ta ci tarar Kamfanin Meta dala miliyan 220

An buƙaci Meta ya biya ƙarin dala 35,000 da Nijeriya ta kashe wajen gudanar da binciken.

Gwamnatin Tarayya ta ci tarar Kamfanin Meta dala miliyan 220

Gwamnatin Nijeriya ta ci tarar Kamfanin Meta dala miliyan 220 kamar yadda shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Masu Sayayya (FCCPC), Adamu Abdullahi ya bayyana.

Cikin sanarwar da Abdullahi ya bayyana a ranar Juma’a ya ce wannan matakin ya yi daidai da dokokin Hukumar FCCPC na 2018 da 2020.

FCCPC ta bayyana ta ce an ci tarar kamfanin ne bayan sakamakon binciken da ƙasar ta gudanar wanda ya gano musayar bayanai da kamfanin ke yi ta kafofinsa na WhatsApp da Facebook sun saɓa wa dokar ƙasar.

Binciken wanda hukumar ta FCCPC tare da Hukumar Kare haƙƙin bayanai (NDCP) suka gudanar a tsakanin watan Mayun 2021 zuwa Disamba na 2023, ya zargi kamfanin Meta da yin amfani da ɗaukar bayanan mutane ciki har da na sirrinsu ba tare amincewarsu ba da kuma mamayar kasuwanci.

Hukumar FCCPC ta kuma bukaci kamfanin ya biya ƙarin dala 35,000 na kuɗaɗen da ta kashe wajen gudanar da binciken.

Gwamnatin Nijeriya ta ba kamfanin wa’adin wata biyu ya biya kuɗaɗen na tara.

Sai dai kawo yanzu babu wani martani da ya fito daga kamfanin.