Gwamnati ta dakatar da harajin shigo da shinkafa da wasu kayan abinci
Gwamnatin ta dakatar da biyan harajin ga ‘yan kasuwa na tsawon kwanaki 150.
Gwamnatin Tarayya ta amince da shigo da muhimman kayan abinci kamar su shinkafa, wake, alkama da masara ba tare da biyan kuɗin haraji ba, domin rage tasirin tsadar kayan abinci.
Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari ne, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.
- El-Rufai da Majalisar Kaduna: Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 17 ga Yuli
- Abuja: Wani mutum ya yi barazanar kashe kansa kan tsadar rayuwa
Ya ce shugaba Tinubu ya amince da janye ƙudin fito kan muhimman kayan abincin ne har tsawon kwanaki 150, domin sauƙaƙa tsadar kayayyakin abinci da ake fama da su.
Wannan wani ɓangare ne na tsare-tsaren shugaban ƙasa na nufin daidaita tattalin arziƙi da samar da abinci a faɗin ƙasar nan.
Ministan, ya bayyana irin ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na yaƙi da hauhawar farashin kayan abinci.
Tsada da matsin rayuwa ya ƙaru tun bayan da Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
A sannu kayan masarufi suka tashin gwauron zabi a Najeriya, lamarin da ya kai wasu yankunan irin su Kano, Neja, Katsina, Jigawa, Legas da wasu yin zanga-zanga da adawar tashin kayan abinci.
Gwamnati za ta shigo da alkama da masara daga waje
Sanarwar ta ce baya ga janye ƙuɗin fito ga ’yan kasuwa masu buƙatar shigo da kayan abinci.
Har wa yau, Gwamnatin Tarayya za ta shigo da alkama kimanin tan dubu 250 da masara tan 250 da za ta bai wa kamfanoni jihohi da ke sarrafa su.