Gwamnatin Tarayya ta fara gina gidaje 500 a Kano
Ministan ya buƙaci ɗan kwangilar ya zage damtse domin kammala aikin a kan lokaci.
Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane ta Tarayya, ta fara gina gidaje 500 a Jihar Kano.
Aikin ginin gidajen da aka yi wa laƙabi da “Renewed Hope Estate” na wakana ne a ƙauyen Lambu da ke ƙaramar hukumar Tofa.
- Ta’aziyyar Sarkin Ningi: Bangon jingina ya faɗi
- Ambaliya ta lalata gidaje 2,517 da hektar gonaki 1,000 a Gombe
Aikin ya haɗa da gina gida mai ɗaki biyu, ɗaki ɗaya, da kuma waɗanda ke da ɗaki uku.
A lokacin da ya kai ziyara wajen aikin, Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aikin ke tafiya.
Ya ce aikin ba ya sauri kamar yadda aka tsara tun da fari.
Ya gargaɗi wanda aka bai wa kwantiragin da ya hanzarta ko kuma gwamnat ta ƙwace aikin daga hannusa.
“Ba mu gamsu da yadda aikin ke tafiya ba. Ya kamata a ce aikin ya yi nisa a yanzu. Idan har ba a samu ci gaba ba nan da mako mai zuwa, za mu karɓi aikin, mu bai wa wani.
“Mun zaɓe ku ne saboda mun yarda da ƙwarewarku. Mutane da dama na neman wannan kwangilar aikin. Kuna buƙatar ƙara ma’aikata saboda ana sa ran kammala aikin cikin watanni biyar. Muna son ganin an kammala aikin nan da ƙarshen shekara.”
Kwantiragin, wanda manajan aikin Haruna Lawal ya wakilta, ya bai wa ministan tabbacin cewa za su ƙara ƙwazo don ganin sun kammala aikin kafin cikar wa’adin da aka ɗebar musu.