Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan 4.3
A Larabar da ta gabata Gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan 4.3 a zauren Majalisar Tarayya da ke Abuja.Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iweala ce ta gabatar da kasafin kudin na badi, inda ta yi hasashen za a kashe Naira tiriliyan 4.3.Gwamnati ta yi kasafin kudin ne bayan ta rage kudin gangar […]
A Larabar da ta gabata Gwamnatin tarayya ta gabatar da kasafin kudi na Naira tiriliyan 4.3 a zauren Majalisar Tarayya da ke Abuja.
Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iweala ce ta gabatar da kasafin kudin na badi, inda ta yi hasashen za a kashe Naira tiriliyan 4.3.
Gwamnati ta yi kasafin kudin ne bayan ta rage kudin gangar danyen mai da ta yi niyya a kasafin tun a farko daga Dala 78 zuwa 65 saboda faduwar farashin mai da faduwar darajar Naira.
Ta ce: “Mun bar kudin a haka ne saboda muna sa ran a shekara mai zuwa matsakaicin farashin da za a sayar da gangar danyen mai ba zai wuce Dala 65 zuwa 70 ba.”
Ta ce Najeriya na hako gangar danyen mai miliyan 2.2 a kullum, inda ta yi fatan cike gibin kasafin kudin daga kudin shigar da za a samu daga wasu bangarori da ba na mai ba.
Kafar yada labarai ta Premiumtimes ta rawaito Shugaba Jonathan Goodluck cewa ya tura Ministar Kudi ce sakamakon rashin sanin abin da zai je ya zo a majalisar a lokacin da zai gabatar da kasafin da kansa, kasancewar ’yan majalisar na jin haushin shi, inda suka zarge shi da sanya ’yan sanda su jefa wa Shugaban Majalisar Tarayya, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal tiya gas.
Duk da cewa Jonathan ya ce ba shi ya ba da umarni hakan ba amma fadar Shugaban kasa ta ce abin da suka yi bai saba doka ba.
Wasu Sanatoci sun zargi Jonathan da rashin taimaka musu don su samu tikitin tsayawa zabe takara a Jam’iyyar PDP. Lokaci ne kawai zai bayyana ko ’yan majalisa za su amince da kasafin kudin duk da wannan takaddamar.