Gwamnatin Tarayya ta kai manoma dubu 70 kotu
Gwamnatin Tarayya ta kai karar manoma dubu 70 kotu a Jihar Kebbi wadanda suka kasa biyan rancen da suka karba a karkashin shirin noma na Babban Banki Najeriya (Anchor Borrower). Shugaban Kungiyar Manoma Shinkafa ta Najeriya reshen Jihar Neja, RIFAN, Muhammad Sahabi Augie ya bayyana wa manema labarai cewa daga cikin manoma dubu 70 da […]
Tambarin RIFAN
Gwamnatin Tarayya ta kai karar manoma dubu 70 kotu a Jihar Kebbi wadanda suka kasa biyan rancen da suka karba a karkashin shirin noma na Babban Banki Najeriya (Anchor Borrower).
Shugaban Kungiyar Manoma Shinkafa ta Najeriya reshen Jihar Neja, RIFAN, Muhammad Sahabi Augie ya bayyana wa manema labarai cewa daga cikin manoma dubu 70 da suka ci gajiyar rancen a shekarar 2015, manoma 200 ne kacal suka iya biyan bashin.
Muhammad Sahabi Augie wanda ya janyo hankalin jam’iyyar adawa ta PDP kan zargin da take yi, ya ce wadanda aka gurfanar da su a gaban kotun manoma ne, wadanda aka tabbatar kafin a ba su bashin.
Ya ce yin zargi ba bisa ka’ida ba bai dace ba, inda ya ce wadansu da suke cewa bashin da aka bayar ’yan siyasa ne suka yi rub-da-ciki a kai, na iya kawo rashin samun damar cin gajiyar ire-iren wadannan shirye-shirye a nan gaba.
Ya ce kungiyar ta kasa karbo basussukan daga manoma ne, inda suke yanke shawarar kai manoman kotu.