Gwamnatin Tarayya ta kashe N604m wajen sauya halin tubabbun ’yan ta’adda
Sai dai da yawan ‘yan Najeriya sun soki wannan shiri na mayar da tubabbu ‘yan ta’adda cikin al’umma.
Gwamnatin Tarayya ta kashe sama da Naira miliyan 604 wajen gyara hali da kuma mayar da tubabbun ’yan ta’adda cikin al’umma ta hanyar shirin Operation Safe Corridor.
Bayanan da aka samu daga Govspend sun nuna cewa an kashe kuɗin ne wajen gina ɗakunan kwana, ayyuka, da biyan haraji da suka shafi cibiyoyin gyara halin tubabbun ’yan tada ƙayar baya.
- Majalisar Kano ta kafa kwamitin tantance Murtala Garo a matsayin Gataimakin Gwamna
- Ministan Wutar Lantarki ya yi murabus
Daga cikin kuɗaɗen da aka kashe akwai Naira miliyan 47.4 domin aikin tuntuɓa a gidan gyaran hali na Kirikiri da kuma Naira miliyan 41.7 domin ƙarin ginin ɗakunan kwana a Mallam Sidi da ke Jihar Gombe.
Wani babban kamfani mai suna FOSAB Global Energy Service Ltd, ya karɓi sama da Naira miliyan 45 domin gina ɗakunan kwana da cibiyoyin gyaran tubabbu.
Haka kuma an biya harajin VAT da withholding tax ga Hukumar Tara Haraji ta Ƙasa (FIRS).
Gwamnati ta ce ta gyara rayuwar tsofaffin ’yan ta’adda da waɗanda rikicin ta’addanci ya shafa guda 744, ciki har da baƙi takwas daga ƙasashe maƙwabta.
Mafi yawansu daga Jihar Borno suka fito.
Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya ce shirin na da nufin rage tashin hankali da hana tasirin tsattsauran ra’ayi.
Ya ce gyaran ba sassauci ba ne, illa wata hanya ce ta ɗaukar matakan tsaro. Sai dai wasu ’yan Najeriya sun soki wannan tsari.
Mai magana da yawun jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce bai kamata a ɗauki ta’addanci da sauƙi ba, yana mai gargaɗin cewa fifita gyara kan adalci alama ce ta rauni.
Shi ma mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Dakta Omenazu Jackson, ya bayyana shirin a matsayin rashin adalci ga waɗanda abin ya shafa, yana cewa matakin ba tare da ɗaukar hukunci ba yana ƙrfafa rashin hukunta masu laifi.
Duk da wannan, jami’ai sun ce an riga an mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram sama da 5,000 cikin al’umma, kuma babu wanda ya koma ta’addanci cikin watanni shida bayan sakinsa.