Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira biliyan 3 wajen gina dakunan bahaya a makarantu
Gwamnatin Tarayya ta kashe tsakanin Naira miliyan 40 zuwa 50 domin gina dakunan bahaya da na wanka a kowace daya daga cikin makarantunta na hada da ke sassan kasar nan.Binciken jaridar Aminiya ya gano cewa a cikin shekarun nan gwamnatin ta giggina irin wadannan dakunan bahaya da ake yi wa lakabi da ‘bahayan alfarma,” a […]

Gwamnatin Tarayya ta kashe tsakanin Naira miliyan 40 zuwa 50 domin gina dakunan bahaya da na wanka a kowace daya daga cikin makarantunta na hada da ke sassan kasar nan.
Binciken jaridar Aminiya ya gano cewa a cikin shekarun nan gwamnatin ta giggina irin wadannan dakunan bahaya da ake yi wa lakabi da ‘bahayan alfarma,” a makarantun hadakar.
Binciken ya gano ta kashe jimillar Naira biliyan uku da miliyan 100 domin gina dakuna bahaya da na wanka a makarantun sakandaren hadaka 64 a shekarar 2014 zuwa 2015.
Kuma an ware wasu kudin domin yin irin wannan aiki a kasafin kudin bana. Akwai dai makarantun sakandaren hadaka 104 a kasar nan.
Sai dai Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta kare kashe wannan kudi kan dakunan bahayar da cewa an bullo da dakunan bahayar ne domin inganta tsabtar dakunan wanka da dakunan bahaya a makarantun.
Takardun kasafin kudi, sun nuna cewa an kashe wa makarantun Naira biliyan daya da miliyan 450 wajen gina dakunan bahaya a shekarar 2014, yayin da aka kashe musu Naira biliyan daya da miliyan 640 a shekarar 2015.
Bayanan da aka samu daga Ofishin Kasafin Kudi na Tarayya sun nuna cewa kwalejojin hadaka 29 sun kashe Naira biliyan daya da miliyan 450 a shekarar 2014 inda kowacce ta samu Naira miliyan 50. Sai kuma a shekarar 2015, wasu kwalejoj 41 suka samu Naira miliyan 40 kowaccensu, inda jimilla ya kama Naira biliyan daya da miliyan 640.
An gano kwalejoji shida sun ci gajiyar dakunan bahaya na ‘alfarma’ da dakunan wanka sau biyu. Kwalejojin sun hada da Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Sakkwato da takwararta ta Okigwe da Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Bauchi da ta Efon Imnringi da ta Ezzamgbo Abakaliki da kuma ta Ibillo. Kowaccensu ta samu Naira miliyan 50 a shekarar 2014 da Naira miliyan 40 a shekarar 2015 domin yin irin wannan aiki.
Kudin ya fito ne da taken “dakunan bahaya na alfarma da dakunan wanka don dakunan kwanan dalibai da ajujuwa,” kuma Shirin Bunkasa kasa na Muradun karni (MDGs) da yanzu ake kira da shirin Tabbatar da dorewar Bunkasakasa (SDGs), ke kula da aikin. Kuma a karkashin wannan batu dai an tsara aikin samar da dakunan girki na zamani da gyara dakunan cin abinci.
A cikin shekara biyu, daukacin kwalejojin hadaka na kasar nan sun kashe Naira biliyan 12 da miliyan 400 wajen gyara da kawatawa da sauran manyan ayyuka a makarantun.
Makarantun da aka ba kudi don gina bahaya na ‘alfarma,’ sun hada da Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Buni Yadi da ta Garki da Keffi da Ogbomosho da Okigwe da Fatakwal da Rubbochi da Sakkwato da Zariya da billiri da Ikole.
Saura sun hada da Kwalejojin ’Yan mata na Gwamnatin Tarayya na (FGGC) da ke Akure da Bauchi da Efon Imnringi, Enugu da Ezzamgbo Abakaliki da Gboko da Gusau da Ibillo da Ikot-Obio-Itong da Ipetumodu da Jalingo da Kabba da Kazaure da Umuahiya. Sai Kwalejin Kimiyya da kere-kere (FSTC) da ke Awka da Michika da Usi Ekiti da kuma Dayi.
Makarantun da suka karbi Naira miliyan 40 kowaccensu a shekarar 2015 don gina dakunan bahayar na ‘kasaita ko alfarma’ sun hada da FGC Sakkwato da Ganye da Iket Nise da Iket bandakya da Ikot Ekpene da Ikurin da Kaduna da Kano da Kiyawa da Maiduguri da Minna da Odogbolu da Ogoja da Ohafiya da Okigwe da Okposi da Onitsha da Ugwolawo da Ido-Ani da Anka da Bajoga.
Sauran sun hada da FGGC, Bauchi da Bakori da Efon-Alaye da Efon Imnringi da Ezzamgbo Abakaliki da Ibillo da Langtang da Lejja da Omu-Aran da Oyo da kuma ta Yola. Sai FTC Ikare da FTC Ilesha da Kafanchan da Ohanso da Uromi da Zuru da kuma Suleja Academy duk sun amfana. Makarantar FSTC, Jubu-Imushin ce kawai ta samu Naira miliyan 40 a shekarar 2015.
dakunan bahaya na ‘alfarma’ don inganta kiwon lafiya ne – Ma’aikata
Mataimakin Darakta, bangaren Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Ben Bem Goong ya ce, dakunan bahaya na ‘alfarmar’ an bullo da su ne don inganta tsabtar dakunan wanka da na bahaya a makarantun. Ya ce, dakunan bahayar suna da araha kuma suna da kayayyakin da suka dace da kananan yara kuma suna rage hadarin yada cututtukan da ke yaduwa. Ya ce dakunan bahayar ba su rike ruwa kamar sauran dakunan bahaya domin kauce wa watsuwar ruwan a jiki.
Ya ce kimanin dakunan bahaya biyar zuwa bakwai aka gina a kowace makaranta tare da tankin adana ruwa na sama domin samar da ruwan tura bayi.
Nazarin ya gano cewa a shekarar 2014, kwalejojin hadaka na kasar nan sun kashe Naira biliyan takwas da miliyan 818 kan manyan ayyuka domin gyara da kawata gine-gine. Kuma baya ga dakuna bahaya na ‘alfarma’ daukacin kwalejojin hadakar na kasar nan an ware musu kudin yin gyare-gyare da kawata makarantun da aka ba su mafi karanci Naira miliyan 50, mafi yawa Naira miliyan 450.
Kwalejojin FGGC Gumi da Tambuwal sun samu Naira 450; FSTC Ekiti, Naira miliyan 142; FGC Ipetumodu Naira miliyan 133 da kuma FSTC Michika wadda ta samu Naira miliyan 132.
Wakilanmu sun ruwaito cewa makarantun hadaka 23 sun karbi Naira miliyan 50 kowacce don yin manyan ayyuka, sai 43 da suka karbi Naira miliyan 75 kowacce, yayin da 12 suka karbi Naira miliyan 125 kowacce.
Sannan makarantun hadaka 13 sun kashe Naira miliyan 100 kan manyan ayyuka a daidai lokacin da makarantu bakwai suka karbi Naira miliyan 82 domin wannan manufa.
Sauran ayyukan da suka bayyana a kasafin kudin makarantun sun hada da kammala ginin katanga da gina ajujuwa da rukunin ofisoshi da dakunan kwanan dalibai.
A shekarar 2015, makarantun hadaka 104 na kasar nan sun kashe Naira biliyan 3 da miliyan 600 kan gina dakunan bahaya da dakunan cin abinci da katange makarantun da sauransu, kamar yadda nazari kan kasafin kudin makarantun ya nuna.
Kuma an gano kashi 90 cikin 100 na kwalejojin da suka hada da FSTC da FSC dukkansu an ba su Naira miliyan 13 da rabi kowaccensu.
Kudin a bisa dalla-dallar bayanin kasafin da muka samu a shafin intanet na Ofishin Kasafi na Tarayya an yi amfani da su ne wajen gina dakunan jinya da dakunan karatu da hanyoyi da dakunan ma’aikata da ajujuwa.
Kuma yayin da FGC Sakkwato take kan gaba wajen samun kudin gini da gyara a shekarar 2015 inda ta samu Naira miliyan 66 da rabi, FGGC Jalingo da King’s College da kueen’s da FGGC Gboko da wasu 36 sun samu Naira miliyan 13 da rabi-rabi ne0.
kueen’s College ta samu kaso mafi tsoka a baya da ya kai Naira miliyan 621, sai FTC Yaba ke biye da ita da Naira miliyan 606, yayin da FGC Ijanikin, Legas ta zo ta uku da Naira miliyan 562.
Binciken ya nuna cewa FSTC Dayi a Jihar Katsina ce ta zamo kutal a kason shekarar 2015 da kimanin Naira miliyan 118.
Sannan kowacce daga cikin kwalejojin hadakar ta samu abin da ya kama daga Naira miliyan 40 zuwa 70 domin bayar da tallafin abinci, kuma hakan ya bayyana ne a kudaden da makarantun suka kashe. Sannan aikin feshi da shara a kowace makaranta ya ci daga Naira dubu 500 zuwa Naira miliyan daya.
Kuma nazarin kasafin bana ya nuna cewa kudin da Majalisar Dokoki ta kasa ta amince don bai wa makarantun hadakar 104 sun kai Naira biliyan 14 da miliyan 300, kuma galibi za su tafi ne ga gyara da sake gina ajujuwa da samar da wutar kan hanya da gina katanga da sayen motoci da sauransu.
Makarantar da ta fi samun kaso ita ce FGC Buni Yadi da ke Jihar Yobe, wadda aka ware mata Naira miliyan 962 da dubu 500 a kasafin na bana. An kashe dalibai da dama a wannan makaranta yayin da aka kone galibin ginin makarantar a lokacin da mayakan Boko Haram suka kai mata hari a shekarun baya.