Gwamnatin Tarayya ta mayar wa Obasanjo da martani
Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammed ta mayar wa Obasanjo da martini a kan wasikar da ya aike wa Shugaban Kasa Buhari inda ya bukaci Buhari ya hakura da tsaya wa takara a zaben 2019. A martanin mau dauke da shafi 7 da minsiyan ya fitar ga manema labarai na fadar […]
Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammed ta mayar wa Obasanjo da martini a kan wasikar da ya aike wa Shugaban Kasa Buhari inda ya bukaci Buhari ya hakura da tsaya wa takara a zaben 2019.
Minstan ya kara da cewa wajibi ne a yaba wa Buhari kan abubuwa biyu cikin ukun da aka yi wa jama’a alkawari a lokacin yakin neman zabe, wato yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da ta’addanci. Sannan kuma ya nuna cewa yanayin yadda aikace-aikacen suka yi wa Obasanjo yawa ya sa "bai samu damar fahimtar ci gaban da gwamnatin Buhari take samu ba a halin yanzu a fannin bunkasa tattalin arziki."
Ministan ya ce kasar ta fita da matsin tattalin arziki, sannan kuma hauhawan farashin kayayyaki ya ragu da kashi 15 cikin 100 a wata 11 a jere.