Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Amurka kan cin zarafin Kiristoci 

Amnesty International ta ce matsalar tsaro ta fi shafar Musulmi maimakon Kiristoci a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin Amurka kan cin zarafin Kiristoci 

Gwamnatin Tarayya ta musanta zargin da wani ɗan majalisar Amurka, Chris Smith, ya yi cewa ana tauye wa Kiristoci ’yancin addini a Najeriya.

Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta ba su da alaƙa da addini, domin hare-haren ’yan ta’adda na shafar dukkanin Musulmi da Kiristoci.

Tuggar ya ce hare-haren da ake kai wa a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ba sa ware mabiyan wani addini.

Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa kan yadda ake yaɗa rahotannin da ba su dace ba, waɗanda ka iya haddasa rarrabuwar kawuna a ƙasar.

Rahoton wata ƙungiya mai suna Open Doors ya ce kashi 89 na Kiristocin da ake kashewa a duniya na faruwa ne a Najeriya.

Sai dai ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta musanta hakan, inda ta ce Musulmi ne ma aka fi kashewa a tashe-tashen hankulan da ake fama da su.

Tun a zamanin mulkin Trump, Amurka ta saka Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake zargin suna tauye ’yancin addinin Kiristoci.

Sai dai Gwamnatin Tarayya ta ce wannan batu ba shi da tushe balle makama.