Gwamnatin Tarayya ta nada shugabannin hukumomin ilimi 17
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin shugabannin hukumomin ilimi 17 da suke karkashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.Wadanda aka nadan sun hada da tsohon Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Abubakar Rasheed a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) da Lilian Salami ta Cibiyar Tsarawa da Kula da Ilimi ta […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin shugabannin hukumomin ilimi 17 da suke karkashin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.
Wadanda aka nadan sun hada da tsohon Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Abubakar Rasheed a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) da Lilian Salami ta Cibiyar Tsarawa da Kula da Ilimi ta Najeriya (NIEPA) da tsohon Daraktan Gidan Arewa Dokta Hameed Bobboyi na Hukumar Kula da Ilimi Bai-daya (UBEC) DA Lanre Aina na Hukumar Kula da dakunan Karatu ta kasa (NLN) da Charles Uwakwe na Hukumar Jarrabawar Sakandare ta kasa (NECO) da Abba Haladu na Hukumar Yaki da Jahilci da Ilimin Manya ta kasa da Bashir Usman na Hukumar Ilimin Makiyaya ta kasa (NEC) da Misis Ifeoma Isiugo-Abanihe ta Hukumar Ilimin Sana’o’i da kere-kere, (NABTEB).
Sauran su ne Sunday Ajiboye na Hukumar yi wa Malaman Makaranta Rajista ta Najeriya (TRCN) da Afolabi Aderinto na Hukumar Rajistar Kwamfuta ta Najeriya (CRCN) da Bappah Aliyu na Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi ta kasa (NCCE) da Farfesa Abdullahi Bichi Baffa na Asusun Kula da Manyan Makarantu (TETFund) da Dokta Garba Dahuwa Azare na Cibiyar Ilimi ta kasa (NTI) da kuma Michael Afolabi na Hukumar Rajistar dakunan Karatu ta kasa (LRCN).
Sannan an nada Steben Ejugwu Onah a matsayin Shugaban Cibiyar Ilimin Lissafi ta kasa da (NMC) da Farfesa Ishak Oloyede na Hukumar Siryar Jarrabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu ta kasa (JAMB) da Misis Chinyere Ohiri-Aniche ta Cibiyar Ilimin Harsunan Najeriya ta kasa (NINL).
Wata sanarwa da ta fito daga wani darakta a ma’aikatar Mista Benjamim Goong, ta ce hudu daga cikin shugabannin wasu hukumomin sun koma kan kuherunsu da suka hada da Sama’ila Junaidu Hukumar Bincike da Bunkasa Ilimi ta Najeriya (NERDC) da Ra’ufu Adebisi na kauyen Koyar da Harshen Faransanci da ke Badagry a Jihar Legas da Dokta Mas’ud A. Kazaure na Hukumar Ilimin kere-kere (NBTE) da Muhammad Mu’az na kauyen Koyar da Harshen Farasanci da ke Maiduguri a Jihar Borno.
Sababbin shugabannin hukumomin sun gana da Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu a harabar ma’aikatar a ranar Talatar da ta gabata.