Gwamnatin Tarayya ta ninka kudin makarantar daliban sakandire
An yi wa sabbin dalibai karin kashi 122 a kudin makaranta.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da karin fiye da kashi 100 na kudin makarantar sabbin daliban sakandire da ke karkashinta da aka fi sani da Unity Colleges ko kuma Federal Government College (FGC).
Da wannan lamari, a yanzu sabbin dalibai za su rika biyan N100,000 sabanin N45,000 da sabbin dalibai na bara suka biya.
- Tallafin N8,000 zai biya bukatun iyalai da dama — Gwamnan Nasarawa
- Matata ce ta sa ni bidiyon barkwanci – Bello Galadanci
Hakan dai na kunshe cikin wata takarda mai lamba ADF/120/DSSE/I da aka fitar daga Ofishin Daraktar Kula da Makarantun Sakandire a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Hajiya Binta Abdulkadir.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, karin kudin zai shafi duk ababe da harkokin karatun daliban ciki har da kudin kwana, littafai na rubutu da karatu, kayan makaranta, wasanni da sauransu.