Gwamnatin tarayya ta rage kashi 50 na kudin wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya ta sanar da rage kashi 50 cikin 100 na kudin wutar lantarki. Hukumar da ke kayyade kudin wutar lantarki ta Najeriya a ranar Larabar makon jiya ta bayyana yiwuwar rage kudin wutar da kashi 50 cikin 100.Shugaban hukumar Sam Amadi ne ya sanar da rage kudin wutar a ranar Talata a Abuja, inda […]

Gwamnatin tarayya ta rage kashi 50 na kudin wutar lantarki
Gwamnatin tarayya ta rage kashi 50 na kudin wutar lantarki

Gwamnatin Tarayya ta sanar da rage kashi 50 cikin 100 na kudin wutar lantarki.

Hukumar da ke kayyade kudin wutar lantarki ta Najeriya a ranar Larabar makon jiya ta bayyana yiwuwar rage kudin wutar da kashi 50 cikin 100.
Shugaban hukumar Sam Amadi ne ya sanar da rage kudin wutar a ranar Talata a Abuja, inda ya bayyana sabon kudin wutar zai fara amfani a karshen watan nan (Maris).
Mista Amadi ya ce tun bayan da gwamnati ta amince da sabon tsarin kudin wutar lantarki a watan Janairu, 2015, hukumarsu ta samu korafe-korafe da rubuce-rubuce daga wurin jama’a, inda suka nuna adawa da sabon tsarin da kai tsaye ya fi shafar jama’ar da ke amfani da wutar lantarki a gidajensu.
Ya bayyana korafe-korafen da suka samu daga masana’antu a karkashin kungiyar masana’antu ta Najeriya kan a rage kudin wutar lantarkin ya sanya suka sake duba tsarin biyan kudin wutar.
Ya ce, kungiyar ta bayyana karin kudin wutar ba zai haifar musu da kuma kasar nan da mai ido ba, domin farashin komai zai tashi, sannan jama’a da dama za su rasa aikin yi.
Hakan ya sanya suka kara duba al’amarin, sannan suka tuntubi kwastomomi don su fahimci kudin da za su iya biya.
Ya ce ba su rage kudin wutar ba sai da suka tuntubi shugabannin kamfanonin da suke rarraba wutar lantarki a kasar nan.
“Mun rage kudin wuta ne bisa dokar samar da wutar lantarki da aka samar a shekarar 2005, wadda ta bada damar a duba yiwuwar rage kudin wuta kasa da kwanaki 60 bayan turo korafe-korafen da ke bukatar yin hakan.”