Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin tallafin karatun ɗaliban da ke ƙetare

Wasu daga cikin ɗaliban sun koka kan rashin biyansu kuɗin alawus na tsawon watanni.

Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin tallafin karatun ɗaliban da ke ƙetare

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman

Gwamnatin Tarayya ta rage kuɗin tallafin karatu ga ɗaliban Nijeriya da ke karatu a birnin Moscow na ƙasar Rasha.

Gwamnatin ta rage kuɗin tallafin daga dala 5,650 zuwa dala 4,370, kamar yadda wata takarda daga Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta wallafa.

A cewar sanarwar da aka fitar a madadin Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, matakin ba zai shafi tallafin lafiya da kuma inshorar lafiya da kuɗin tafiya karatun ba.

Kuma a cewar takardar, gwamnatin ta rage yawan kuɗaɗen ne saboda dalilai na matsalar tattalin arziki.

Gwamnatin Najeriya dai ta tura ’yan ƙasarta zuwa wasu ƙasashe karatu ƙarƙashin wata yarjejeniyar ilimi tsakaninta da ƙasashen na ƙetare.

Sai dai wasu daga cikin ɗaliban sun koka kan rashin biyansu kuɗin alawus na tsawon watanni, lamarin da Gwamnati ta ce tana shirin yi wa tufkar hanci.

Shekararu da tawagarsa sun yi watsi da tsarin rabon haraji

An lalata turakun wuta 18 cikin kwanaki 5 a Najeriya — TCN

Sibil Difens ta kama mutum 10 kan aikata laifuka daban-daban a Gombe

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe