Gwamnatin Tarayya ta sake ba jihohi tallafi ko ta kyale su?
Bai kamata ba – A’isha Mukhtar Daga Zainab Mukhtar, Abuja Aisha Mukhtar: “Bai kamata Gwamnatin Tarayya ta rika diban kudi tana ba gwamnatin jihohi ba saboda yin hakan na nuna kamar an sakar musu ragama su rika facaka da kudin Gwamnatin Tarayya. Jihohi da dama duk da kudaden da aka ba su, kuma aka ba […]
Bai kamata ba – A’isha Mukhtar
Daga Zainab Mukhtar, Abuja
Aisha Mukhtar: “Bai kamata Gwamnatin Tarayya ta rika diban kudi tana ba gwamnatin jihohi ba saboda yin hakan na nuna kamar an sakar musu ragama su rika facaka da kudin Gwamnatin Tarayya. Jihohi da dama duk da kudaden da aka ba su, kuma aka ba su shawara su biya ma’aikata, har yanzu ba su biya basukan watannni da ake binsu ba. Ta yaya za a ce yin tituna ya fi biyan hakkin mutane? Mutanen nan mafi yawansu abinci ma ya gagare su, ballantana kudin makarantar ‘ya’yansu. Kamata ya yi jihohi su nemi yadda za su yi su biya ma’aikatansu da kansu tun da dama su aka yi wa aiki ba Gwamnatin Tarayya ba. domin kuwa ko an kara ba su, ba lallai ba ne su biya ma’aikatan ba.”
Ya dace a sake tallafa musu- Alhaji Alhassan Jega
Daga Abbas Ɗalibi, a Abekuta
Alhaji Alhasan Jega: Magana ta gaskiya ya kamata Gwamnatin Tarayya ta rika bibiyar abin da jihohin ke yi da tallafin da ake basu, wannan hakki ne na Gwamnatin Tarayya, kuma shi ne abin da in anyi zai amfani talaka, kin basu tallafin ba zai haifar wa talaka alheri ba. Don haka sake basu tallafin shi ya fi cancanta, amma an rika bin diddigin yadda suke batar da kudin.
Tallafa musu ya fi alheri – Hajiya Ummi Muhammad
Daga Abbas Ɗalibi, a Legas
Hajiya Ummi Muhammad: Eh ya kamata Gwamnatin Tarayya ta sake bai wa jihohi tallafi domin in bata tallafa masu ba, abin da suke samu ba zai ishe su ba. Don haka a tallafa masu ya fi alheri kuma hakki ne da ya rataya a wuyan shugaban kasa ya tabbatar ana bibiyar aikin da suke yi da tallafin da aka basu, amma in an hana su ai zasu fake ne da guzma su harbi karsana.
Ba na goyon baya – MB Musa Paki
Isiyaku Muhammed
MB Musa Paki: “A ra’ayina ba na goyon bayan Gwmnatin Tarayya ta ba gwamnoni ragowar kashi tallafin kudin Paris club. Duba da wanda aka ba su don su biya basussuka, aikin raya kasa da samar da canji da ayyukan yi, wanda shi ne alkawarin gwamnatin jam’iyyar APC. Idan mu ka yi amfanin da abin da muka gani a kasa, zan iya cewa babu jihar da ta yi amfani da abin da ya kai kashi 25 na kudin. Domin har yanzu akwai matsalar rashin biyan albashi, lallacewar makarantu musamman na firamare, da koma bayan da ake samu a harkar lafiya wanda ya kawo karuwar mutuwa da mata masu juna biyu sukeyi. Daga lokacin da aka ba da kashin farko aka ce su biya basussuka zuwa na biyu, har yanzu ba a magance matsalar komai ba, an samu wata jihar da wasu daga cikin kananan hukumominsu ke ba da albashin kashi 75% da sunan daga baya za a biya ragowar. Wannan ya nuna cewa maimako biyan bashi, kara cin bashin ma suke yi, da wannan nake cewa bana goyon baya.”
Ya kamata a ba su – Ya’u Sani
Isiyaku Muhammed
Ya’u Sani: “Ya kamata a basu domin a gaskiya mu dai a Jihar Kaduna, Gwamna El-Rufai ya samar mana da ayyukan cigaba kamar tsaro, ilimi, tituna, ruwan shad a kuma magance ‘yan ta’adda a cikin birane da kauyukan jihar. Mun gani mun shaida.
Hakanan kuma, a Kaduna, gwamnan ya yi kokari wajen samar da ayyuka ga mutanen jihar, da kuma yadda yake gayyato mana ‘yan kasashen waje suna kafa kamfanoni a jihar, wanda hakan ya taimaka matuka wajen magance matsalar tsaro. Duk wadannan ayyukan gwamna ya yi su ne saboda kudaden da yake samu, kuma ni shaida ne saboda ni kwamanda ne na Jarumai da Gora masu maganin ta’addanci da samar da tsaro a Hayin Banki da kewaye.”
Abu ne mai kyau -Abubakar Sadik Isah
Daga Zainab Mukhtar, Abuja
Abubakar Sadik Isah: “kara wa jihohi kudi domin su samu su biya albashi abu ne mai kyaui, ganin yadda ma’aikata ke shan wahala saboda rashin albashi. Jihohi da dama sun yi watanni babu albashi, kuma akwai abubuwa da yawa da ke bukatar a kula da su. Shi ya sa kudaden da aka basu a baya basu ishe su ba. Hakan ne ya sa ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kara musu kudi domin su karasa biyan albashin da ake binsu, musamman ma irin jihohin da ba sa iya biyan albashin mafi karanci na dubu 19, kamar Jihar Zamfara.”