Gwamnatin tarayya ta tallafa wa Kannywood da Naira miliyan 40

A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sake tallafa wa masana’antun fina-finan Najeriya wadanda suka hada da ta Nollywood da ta Kannywood da kuma ta fina-finan Yarabawa da Naira biliyan 2.Masana’antar fina-finan Hausa wadda aka fi sani da Kannywood ta samu tallafin Naira miliyan 40.Idan ba a manta ba shekara 4 da ta […]

Gwamnatin tarayya ta tallafa wa Kannywood da Naira miliyan 40
Gwamnatin tarayya ta tallafa wa Kannywood da Naira miliyan 40

A makon jiya ne Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya sake tallafa wa masana’antun fina-finan Najeriya wadanda suka hada da ta Nollywood da ta Kannywood da kuma ta fina-finan Yarabawa da Naira biliyan 2.
Masana’antar fina-finan Hausa wadda aka fi sani da Kannywood ta samu tallafin Naira miliyan 40.
Idan ba a manta ba shekara 4 da ta gabata ne shugaban kasar ya fara ba masana’antun fina-finan kasar nan tallafin Naira biliyan 3 karkashin shirin Project Act Nollywood don masu ruwa da tsaki a cikin masana’antun su inganta harkokinsu.
Shirin na wannan karon da aka kira ‘Film Production Fund’, shiri ne na gwamnatin tarayya karkashin Ma’aikatar Kudi ta tarayya, inda ta ware Naira biliyan 2 don ba ’yan fim don su kara inganta harkar fim a Najeriya.
Shugaban Kwamitin da ya shafi wannan shiri a bangaren masana’antar fina-finan Hausa, Saleh Muhammad Ofisa ya bayyana Kannywood ta amfana da tallafin Naira miliyan 40.
Ya ce: “Kannywood ta amfana da horarwa a nan Najeriya da kuma kasar waje, inda mutum 19 suka je Indiya, an kuma horar da mutum 30 a wata makarantar koyon shirya fim mai suna Pillars Training Institute da ke Kano, sannan an horar da mutum 10 a Legas, daga nan ne aka shiga rukunin bada kyautar kudi a Turance Film Production Fund don shirya fim, inda mutane 6 suka amfana. A takaice miliyan 40 ta shigo Kannywood. Wannan kudin kyauta aka bayar don a shirya fim.”
Ya yi korafin sauran masana’antun da suke kudancin kasar nan sun fi amfana da shirin.
Ya ce: “A gaskiyar magana idan ka kalli kudin da aka raba, to an fi kwararmu, domin na duba jerin sunayen wadanda suka amfana da shirin sai na fahimci ’yan kudanci sun fi mu morewa. A bangarenmu, mutum shida suka amfana. Na Nollywood kusan mutum 30, na Yarabawa fiye da 10.”
Batun ko Kannywood ta yi korafi a kan hakan sai ya ce, “ni ne na shige gaba wajen yi wa jama’a fadi-tashi don ganin an ba su tallafin, amma daga karshe ni ban samu ba, saboda wasu dalilai na siyasa, sannan mun yi ta surutu a kan maganar, muka ce irin tallafin da aka ba ’yan Kudu a lokacin da za su je kwas a Amurka ba irinsa aka ba mu ba, na yi rubutu a jaridu. Da aka samu na mutum 6 to a kungiyance ba mu yi korafi ba, tun da za a ci gaba da bada tallafin.”
Ya ce har yanzu ’yan fim za su iya amfana da wannan shirin, “abin da mutum zai yi shi ne ya cika fom, ya bayyana dabarun yadda zai shirya fina-finan Hausa ko dai a ketare ko a nan gida, ko ya bayyana musu sabuwar fasahar da yake da ita don bunkasa kasuwancin fina-finan Hausa, su ma sun ce za su ba shi kudin ya shirya fim. A yanzu muna ta kokari duk wanda ya karbi kudin to ya kashe shi a harkar fim, ba wai ya karkatar da kudin zuwa wani abu daban ba.”
Kamfanonin da suka amfana da wannan shirin daga Arewacin Najeriya sun hada da: karami Multimedia na Abdullahi Sani Abdullahi (Baba karami) da Gyale Productions Limited na Sadiya Gyale da Kumbo Productions Limited na Hajiya Mai Sanafahna da Ramat Production na Balaraba Ramat da Mandawari Enterprise na Ibrahim M. Mandawari da M One Eleben (11) Media Communications Limited da Haszain Global Resources Ltd da kuma benus Media Limited.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa