Gwamnatin Tarayya ta yi tir da kalaman Obasanjo
Gwamnatin Tarayya ta bayyana kalaman tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a kan danganta kungiyar Boko Haram da ISWAP da alaka da Musulunci, wanda yin hakan babban laifi ne da raba kan kasa, kuma wannan kalamai nasa kan iya raba kan kasa,sannan a ce ya fito daga bakin dattijo kamarsa. A sanarwar da Ministan Watsa labarai, […]
Gwamnatin Tarayya ta bayyana kalaman tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a kan danganta kungiyar Boko Haram da ISWAP da alaka da Musulunci, wanda yin hakan babban laifi ne da raba kan kasa, kuma wannan kalamai nasa kan iya raba kan kasa,sannan a ce ya fito daga bakin dattijo kamarsa. A sanarwar da Ministan Watsa labarai, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a Abuja, a ranar Talatar da ta gabata. Ya ce abin takaici ne a ce mutumin da ya yi yaki domin dorewar kasar nan guri daya, shi ne a yanzu yake irin wadannan kalamai da ba su dace ba, wanda hakan kan iya jawo raba kan al’umma.
Ya ce kungiyar Boko Haram da ISWAP, kungiyoyin ta’adda ne, wadanda babu ruwansu da kabila ko addini idan suka tashi kashe-kashensu da bata dukiyoyin al’umma. Ya kara da cewar tun faruwar rikicin Boko Haram, wanda aka fara a kan idon Obasanjo a shekarar 2009, ’ya’yan kungiyar sun fi yawan kashe Musulmi fiye da mabiyan kowanne addini, haka abin yake wajen kona masallatai, fiye da kowanne wuraren ibada, kuma kisan su ba ya zabar kowa, walau kabila ko addini, domin hakan abin takaici ne alakanta kungiyar Boko Haram ko ISWAP da Fulani ko addinin Musulunci.
Alhaji Lai Mohammed ya ce, Shugaba Buhari a jawabinsa, lokacin rantsar da shi a 2015. Ya ce ‘yan kungiyar Boko Haram ba su da imani, babu Allah cikin lamarinsu kuma babu abin da ya hada su da maganar Musulunci, domin sun yi hannun riga da koyarwar Islama.