Gwamnatin Tarayya za ta bude cibiyoyin sayen ma’adanai
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta bude cibiyoyin sayan ma’adanai a jihohin Najeriya don magance fasa kwaurin ma’adanai daga Najeriya zuwa wadansu kasashe. Ministan Tama da karafa Alhaji Musa Muhammad Sada ne ya bayyana haka a lokacin da ya tattauna da wakilan Gwamnatin Jihar Oyo, a karkashin Mataimakin Gwamnan Jihar Moses Alake Adeyemo.Ya ce: “Babbar […]
Gwamnatin Tarayya ta ce za ta bude cibiyoyin sayan ma’adanai a jihohin Najeriya don magance fasa kwaurin ma’adanai daga Najeriya zuwa wadansu kasashe.
Ministan Tama da karafa Alhaji Musa Muhammad Sada ne ya bayyana haka a lokacin da ya tattauna da wakilan Gwamnatin Jihar Oyo, a karkashin Mataimakin Gwamnan Jihar Moses Alake Adeyemo.
Ya ce: “Babbar matsalar da masana’antun sarrafa ma’adanai suke fama da ita kasar nan ita ce fasa-kwaurin ma’adanai daga Najeriya zuwa kasashen ketare. An fi fasa kwaurin ma’adanan kawa (gemstone), inda ake fasa kwaurin kashi 80 cikin 100 na wadannan ma’adanan zuwa kasashen ketare, hakan kuwa abin damuwa ne.’
Ya ce, samar da cibiyoyin da za su rika sayan ma’adanai ne babbar ajandar ma’aikatarsu, inda a yanzu za su fara da kafa cibiyoyi uku. “Bai zama dole sai ma’adanan kawa cibiyoyin za su rika saya ba, ya danganta da ma’adanan da kowace jiha take hakowa.” Inji shi.
Ya yaba wa Jihar Oyo bisa kokarin da take yi wajen bunkasa hako ma’adanai a kasar nan, kasancewar tana da daya daga cikin jihohin da suka mayar da hankali wajen hako ma’adanai, saboda haka ne ya ziyarci jihar sau uku tun bayan da ya zama minista.
“Kashi 70 zuwa 80 cikin 100 na ma’adanan kawa a Jihar Oyo ake hako su, don haka za a samar da cibiya daya a jihar.” Inji shi.
Ya ce, ma’aikatarsu ta gana da masu zuba jari da kungiyar Masu Hakar Ma’adanai ta Najeriya da sauran masu ruwa da zaki a kan harkar ma’adanai, don ganin yadda za a samar cibiyoyin da za su rika sayan ma’adanai.