Gwamnatin Tarayya za ta cika alkawuran da ta yi wa Jigawa – Namadi

Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Muhammad Namadi Sambo ya tabbatar wa gwamnatin Jihar Jigawa cewa Gwamnatin Tarayya za ta cika dukkan alkawuran da ta yi wa jihar a lokacin yakin neman zabe.Mataimakin Shugaban asar ya bayyana haka ne lokacin da yake kaddamar da tashin maniyyata aikin Hajjin bana a filin jirgin sama na Dutse fadar Jihar […]

Gwamnatin Tarayya za ta cika alkawuran da ta yi wa Jigawa – Namadi
Gwamnatin Tarayya za ta cika alkawuran da ta yi wa Jigawa – Namadi

Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Muhammad Namadi Sambo ya tabbatar wa gwamnatin Jihar Jigawa cewa Gwamnatin Tarayya za ta cika dukkan alkawuran da ta yi wa jihar a lokacin yakin neman zabe.
Mataimakin Shugaban asar ya bayyana haka ne lokacin da yake kaddamar da tashin maniyyata aikin Hajjin bana a filin jirgin sama na Dutse fadar Jihar Jigawa.
A makon jiya Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido ya ce ba sa goyon bayan tazarcen Shugaba Jonathan da wasu gwamnonin PDP da suka fito daga Arewa maso Yamma suka bayyana a Kaduna.
Gwamnan ta bakin Mataimakinsa Alhaji Mahmud Gumel ya ce ba za su zabi Jonathan a zabe mai zuwa ba saboda gazawarsa wajen cika wa jihar alkawuran da ya dauka na biyan kudin gina filin jirgin saman da aikin jawo ruwa daga Sintilmawa zuwa Dutse da sauransu.
Da ya juya kan jigilar maniyyatan Alhaji Namadi Sambo ya ce za a sauke su ne kai-tsaye a birnin Madina maimakon Jiddah kuma jirgin Mad Air da ya kwashi maniyyatan zai yi sawu shida ne kafin kwashe na Jigawa.
Ya ce Gwamnatin Tarayya ta nada kwamati mai karfi da zai kula da harkokin alhazan kasar nan a kasa Mai tsarki, inda ya ce gwamnatin ta yi shiri mai kyau don kula da jin dadin alhazan Najeriya a nan gida da Saudiyya.
Y a bukaci maniyyatan Hajjin bana su mayar da hankali wajen yin ibada tare da roka wa kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A jawabin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’adu Abubakar ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan rawar da taka wajen dakile cutar Ebola, lamarin da ya taimaka wajen fara gudanar da jigilar maniyyata aikin Hajjin bana. Ya bukaci gwamnatin ta yi iyakacin kokarinta wajen kawo karshen matsalar Boko Haram kamar yadda ta tashi tsaye wajen yakar Ebola.
A jawabin Amirul Hajjin Bana, Oba na Legas Alhaji Rilwanu Akiodu ya bukaci Gwamnatin Tarayya ne ta kara wa Hukumar Hajji ta kasa kudi domin lura da aikin jigilar maniyyata da tabbatar da tsaro a lokacin aikin Hajjin.
Gwamna Lamido ya gode wa Gwamnatin Tarayya da ta zabi filin jirgin sama na Dutse domin fara jigilar maniyyata aikin Hajji bana daga kasar nan.
Maniyyata 541 ne da suka fito daga Jihar Jigawa suka tashi a karon farko daga filin jirgin saman na Dutse.