Gwamnatin Tarayya za ta hana likitoci aiki a asibitocin kudi

Gwamnatin Najeriya za ta hana likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati yin aiki a asibitocin da aka fi sani da  asibitocin kudi. Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a fadar Shugaban kasa, inda ya ce an tattauna a kan batun a taron Majalisar […]

Gwamnatin Tarayya za ta hana likitoci aiki a asibitocin kudi

Gwamnatin Najeriya za ta hana likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati yin aiki a asibitocin da aka fi sani da  asibitocin kudi.

Ministan Lafiya, Farfesa Isaac Adewole ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a fadar Shugaban kasa, inda ya ce an tattauna a kan batun a taron Majalisar Zartarwa wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewar Ministan, noma ne kawai sana’ar da dokar aikin Gwamnatin Najeriya ta bai wa ma’aikatanta damar yi. Ya ce an kafa kwamitin da zai duba lamarin sannan ya shawarci gwamnati game da yadda za ta yi.

“Majalisar Zartarwar ta dubi lamarin aikin da likitoci ke yi na kashin kansu. Don haka ne aka kafa kwamitin da zai duba lamarin saboda muna so mu yi amfani da abin da dokar kasa ta tanadar da kuma dokar aiki.

“Noma ne kawai sana’ar da dokar kasa ta ba ma’aikacin gwamnati dama ya yi. Don haka kwamitin zai ba gwamnati shawara a kan wannan lamarin,” inji shi.

A nata bangaren, kungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA) ta ce bai kamata a hana likitoci su rika aiki a asibitocin kudi ba. Mai magana da yawun kungiyar, shiyyar Abuja, Dokta Roland Aigbo ne ya sanar da hakan, inda ya ce ya kamata a ce Gwamnatin Tarayya ta shawarci Hukumar Likitoci (MDCN) kafin ta yanke wannan shawarar. Sannan ya ce akwai doka da ta ce likita zai iya aiki na kashin kansa matukar aikin bai shiga lokacin aikinsa ba a asibitin gwamnati.

Su kuma a nasu bangaren, likitoci masu zaman kansu sun yi maraba da wannan dokar, inda suka ce dokar za ta taimaka wajen yin aiki yadda ya kamata. Dokta Frank Odafen, Shugaban kuniyar Likitoci Masu Zaman Kansu (AGPMPN) ne ya sanar da hakan, inda ya ce likitoci masu zaman kansu suna maraba da wannan dokar. “Idan za ka yi aiki na kashin kanka, to ka yi aiki na kashin kanka kawai, idan kuma gwamnati za ka yi wa aiki, to ka tsaya ka yi wa gwamnati aiki. Shin zai yiwu ka tuka mota biyu a tare? Dole sai dai ka tuka daya, ka ajiye daya.