Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?

Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta […]

Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?
Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?

Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta iya hukunta ta kuwa? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban, ga kuma abin da suke cewa:

Ba za a iya hukunta ta ba – Sani Abubakar
Alhaji Sani Abubakar Maitumatir Kasuwar Muda Lawal Bauchi: “Idan da ana hukunta mutane a Najeria da wannan Minista ba za ta yi almubazzarancin sayen motoci kan wannan kudi mai yawa ba, don wannan rashin tausayi ne da rashin tunani nake ganin ya dami wannan mata. Don haka tun da tana da daurin gindi shi ya sa za ta yi wannan aiki saboda sanin ko EFCC sun kama ta ba inda za su yi da ita kuma shi kansa Shugaban kasa, akwai alamun tana da daurin gindi a wajensa; ba zai iya hukumta ta ba. Irin wannan kudi idan da za a hukunta ta da daruruwa ko dubban manyan da ke gwamnati, a amshe kudin a taimaki talakawa wajen kafa masana’antu da; an fita daga halin da ake ciki. Wannan ya sa mu yanzu ko rediyo ba ma ji saboda kullum labarin manyan barayi ya fi yawa kuma ba yadda za a yi da su; daga su sai iyalansu.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya