Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa? (5)
Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta […]
Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta iya hukunta ta kuwa? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban, ga kuma abin da suke cewa:
Gwamnati za ta iya hukunta ta
– Sani Gwamna
Alhaji Sani Gwamna Ahmad Mayanci: “Gwamanati za ta iya hukunta Ministar sufurin jiragen sama bisa sharudda guda biyu, idan za ta raina abin da gwamnati za ta ba ta don sayen motoci kuma a ce ta yi gaban kanta. Ko kuma ta diba cikin lalitar ma’aikatarta, ba tare da izini ba ko sanin gwamnati. Amma tun da ’yan majalisu sun motsa wajen sa kwamitin bincike kan gano inda aka samu kudin kuma hukumar EFCC ta bayyana cewa a shirye take da in dai aka kama ta da laifi, za su hukunta ta; to mun san za ta iya amma sai an fidda son rai.”