Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?(1)

Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta […]

Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?(1)
Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?(1)

Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta iya hukunta ta kuwa? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban, ga kuma abin da suke cewa:

Da wuya ta iya hukunta ta – Abubakar Ibrahim

Abubakar Ibrahim: “Ni aganina, ba abin mamaki ba ne a ce wannan gwamnatin ba za ta iya zartar da wani hukunci a kan Stella Oduah ba saboda wasu manufofi irin wadanda suke mamaye da gwamnatin, domin idan aka yi la’akari ba a kanta hakan ta taba faruwa ba, babu wani shafaffe da mai da aka taba kama shi aka zartar da hukunci a kansa saboda ya aikata wani babban laifi. Don haka ba wani sabon abu ba ne kuma ba abin mamaki ba, idan gwamnati ta kasa zartar da wani hukunci a kanta. Sai dai abin takaici kuma abin bakin ciki ne kwarai, a halin da kasar nan take ciki a ce Stella Oduah ta ware zunzurutun kudi har Naira miliyan N225 domin holewa da jin dadin kanta, ta sayi motocin hawa guda biyu alhali tana sane da halin da wannan ma’aikatar take ciki na yawan hadurra da sauransu.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya