Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?(2)
Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta […]
Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta iya hukunta ta kuwa? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban, ga kuma abin da suke cewa:
Mai yiwuwa a iya hukunta ta – Adamu Bobobo
Adamu Bobobo Sarkin kofar Kasuwar Gwari Bauchi: “Mai yiwuwa a iya hukunta ta idan har kwamitin da aka kafa sun bayar da rahoton a hukunta ta. Saboda wannan gwamnati tana wata irin tafiya ce da ba wanda ya san gabanta sai Allah. Za a iya ganin ba za a hukunta ta ba amma daga karshe idan Shugaba Jonathan ya ga zargi ya yi yawa cikin lamarin sai ya sauke ta don a ji dadin bincike, idan akwai wata almundahanar da ta aikata kan kwangilar gyaran filin jiragen sama da sauran su duk sai dubunta ya cika; ta fito fili. Amma hakika ya kamata a hukunta ta saboda ana ganin mata suna da amana amma yanzu yawanci su ma suna tafka abin da ya fi na maza illa, don haka kullum lamurra lalacewa suke yi a gwamnatin Najeriya. Lamarin sai addu’a.”