Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?(3)

Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta […]

Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?(3)
Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?(3)

Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta iya hukunta ta kuwa? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban, ga kuma abin da suke cewa:

Ba za ta iya hukunta ta ba
 – Haruna Jengebe

Haruna Jengebe: “Ra’ayina shi ne, lallai gwamnati ba za ta iya hukunta ta ba, domin tun da Shugaban kasa ya hau mulki babu wani Minista da aka kama shi da laifi aka hukunta. Don haka minstocin kasar nan, musamman ’yan gaban goshi, wadda ita wannan ministan tana ciki, babu yadda za a yi a hukunta ta, in dai tana yi wa PDP biyayya, domin kowa ya san yadda ta ga dama take yi; babu wanda ya isa ya ce mata ba haka ba. Haka shugabanni da yawa, su ma an kama su da almundahana da facaka da dukiyar al’umma amma babu abin da aka yi masu. Don haka ba za a iya hukun ta ta ba.”

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya