Gwamnatin Tarayya za ta iya hukunta Stella Oduah kuwa?(4)
Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta […]
Tun daga lokacin da tabargazar Ministar Hukumar Sufurin Jiragen Sama, Stella Oduah ta bayyana, Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin daukar matakin hukunta ta, idan an tabbatar da laifinta. Sai dai al’amuran da ke faruwa a kan al’amarin sun fara sa shakku ga zukatan ’yan kasa. Abin tambaya a nan shi ne, ko gwamnatin za ta iya hukunta ta kuwa? Wakilanmu sun tattauna da al’umma daban-daban, ga kuma abin da suke cewa:
Babu abin da gwamnati za ta yi mata
– Muhammadu Gombe
Alhaji Muhammadu Gombe: “A gaskiya Stella Oduah ba ta yi tunani ba da aikata wannan barnar a kan biyan bukatar kanta saboda samun dama kuma abin bakin ciki a nan, babu wani abin da wannan gwamnatin za ta iya yi na hukunta ta ko da an yi wannan binciken an same ta da laifin da ya fi wannan girma. Dalili kuwa, idan aka duba cikin gwamnatin da dama wasu manyan jami’anta suke aikata wannan ruf-da-cikin da ya zarta wannan nata amma gwamnatin ba ta yi komai ba sai kawai maganar ta kare da sunan an kafa kwamitin bincike. A hakan za ta kare ba tare da ta gurfanar da masu aikata ta’annatin ba a gaban kotu kuma ba don komai ba illa kasancewar ire-irensu duk ’yan gaban goshin ita gwamnatin ne.”