Gwamnatin Tarayya za ta maka Daily Trust a kotu kan rahoton Samoa

A cewar jaridar wasu sassan yarjejeniyar, sun buƙaci ƙasashe masu tasowa da su tallafa wajen kare haƙƙin ’yan luwaɗi da ’yan maɗigo (LGBTQ), don ƙara samun tallafi daga ƙasashen duniya. 

Gwamnatin Tarayya za ta maka Daily Trust a kotu kan rahoton Samoa

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin gurfanar da Jaridar Daily Trust a gaban kotu, game da rahoton rattaba hannu kan yarjejeniyar Samoa da ta yi. 

A cewar jaridar wasu sassan yarjejeniyar, sun buƙaci ƙasashe masu tasowa da su tallafa wajen kare haƙƙin ’yan luwaɗi da ’yan maɗigo (LGBTQ), don ƙara samun tallafi daga ƙasashen duniya.

Wannan rahoto dai ya janyo cece-kuce a tsakanin malamai, masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam, da kuma ƙungiyoyin masu zaman kansu a Najeriya.

Aminiya ta ruwaito yadda ran ire-iren waɗannan ƙungiyoyi ya ɓaci, inda suka caccaki Gwamnatin Tarayya kan sanya hannu kan yarjejeniyar.

A martaninsa, Mohammed Idris, ministan yaɗa labarai, ya bayyana cewa duk wani ɓangare na yarjejeniyar da ya ci karo da dokokin Najeriya ba zai yi aiki ba.

Ya nanata cewa Najeriya na da dokar da aka kafa a shekarar 2014, don yaƙi da auren jinsi da duk wani abu da ke da alaƙa da ita.

A yayin ganawa da manema labarai, Idris ya yi Allah-wadai da rahoton na Daily Trust, inda ya bayyana shi a matsayin “mara tushe da nagarta.”

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya, ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, tana da kyakyawar alaƙa tsakaninta da ‘yan jarida tare da goyon bayan ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Sai dai ya nuna damuwarsa kan rahoton wanda ya ce yana barazana ga tsaro da zaman lafiyar ƙasar nan.

Idris, ya zargi jaridar Daily Trust da yi wa Gwamnatin Tarayya ƙazafi wajen sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta bai wa ’yan luwaɗi da ’yan maɗigo damar cin gashin kansu, inda ya bayyana cewar babu wani abu mai kama da hakan a cikin yarjejeniyar.

Ya soki jaridar da rashin iya aiki da kuma tantance haƙiƙanin gaskiya kafin bayyana sakamakon rahotonta.

Sai dai ya ce Gwamnatin Tarayya ta shirya tsaf don maka Daily Trust a gaban kuliya don bin kadun ƙazafin da ta mata.

Gwamnatin Tarayya za ta kai ƙara ga hukumar NPAN a hukumance tare da neman haƙƙinta a gaban kotu.

Yayin da gwamnati ke goyon bayan kafafen yaɗa labarai da ’yancin faɗin albarkacin baki, a gefe guda ya ce gwamnatin ba za ta amince da labaran ƙarya da za su iya yin barazana ga zaman lafiya da tsaron ƙasa ba.

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Yadda mutanen Jigawa suka ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi 

Za mu yi wa Kwankwaso ritaya a 2027 — Doguwa

’Yan daba sun ƙone ofishin hukumar zaɓen Akwa Ibom