Gwamnatin Tarayya za ta nemi diyyar dukiyoyin da ’yan Najeriya suka bari a Afirka ta Kudu

Wasu daga cikin waɗanda suka dawo sun ce sun bar kasuwanci da dukiyoyinsu domin tsira da rayukansu.

Gwamnatin Tarayya za ta nemi diyyar dukiyoyin da ’yan Najeriya suka bari a Afirka ta Kudu

Gwamnatin Tarayya ta ce za ta nemi diyya kan kadarori da kasuwancin da ’yan Najeriya suka bari a Afirka ta Kudu yayin da suke dawowa gida sakamakon hare-haren ƙyamar baƙi.

Muƙaddashin Babban Jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Alexander Ajayi, ya ce gwamnati ta fara tattara bayanan kadarorin da waɗanda suka dawo suka bari, domin tattaunawa da gwamnatin Afirka ta Kudu kan yiwuwar biyan diyya.

Ya ce ba wai dawo da ’yan Najeriya gida kaɗai gwamnati ta sa a gaba ba, har da kare jarin da suka yi a ƙasar.

Ajayi ya kuma musanta zargin cewa yawancin ’yan Najeriya da ke Afirka ta Kudu ba su da takardun zama, yana mai cewa da dama sun shiga ƙasar bisa ƙa’ida, amma suka fuskanci jinkiri wajen sabunta takardunsu.

A halin da ake ciki, wasu ƙarin ’yan Najeriya 271 sun iso Legas daga Afirka ta Kudu a wani ɓangare na shirin dawo da ’yan ƙasar gida.

Wasu daga cikin waɗanda suka dawo sun ce sun bar kasuwanci da dukiyoyinsu domin tsira da rayukansu, tare da gargaɗin ’yan Najeriya da su yi taka-tsantsan kafin su yanke shawarar komawa a Afirka ta Kudu.