Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata rishon girki

Mata da kananan yara 90,000 na mutuwa duk shekara a sanadiyar hayakin itace.

Gwamnatin Tarayya za ta raba wa mata rishon girki

Aishatu Musa Dalil

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na raba wa matan aure rishon girki a duk fadin kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar.

Ministan Harkokin Mata, Pauline Tallen ce ta sanar da hakan ranar Laraba yayin kaddamar da taron kwanaki hudu wanda Hukumar Makamashi ta Kasa (ECN) ta shirya domin fadakar da mata a kan hatsarin da ke tattare da amfani da itace wajen girke-girke.

Aminiya ta ruwaito cewa, an kaddamar da taron ne a kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na rage matsalolin da ke tattare da yawan amfani da itacen girki ga mata.

Da take gabatar da jawabai, Ministar ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari godiya da ya amince a raba rishon girki guda 1000 a kowace karamar hukuma da ke fadin kasar.

Ministar ta ce Shugaba Buhari ya yi la’akari da hatsarin da mata ke fuskanta da yawan wadanda ke mutuwa duk shekara saboda shakar hayakin itace wajen girke-girke.

A cewarta, hakan zai kuma taka rawar gani a fafutikar da mahukunta ke yi wajen magance matsalar sauyin yanayi da ake fama da ita a nan gida Najeriya da sauran sassa na duniya.

Ana iya tuna cewa, a watan da ya gabata ne Karamar Ministar Mahalli, Sharon Ikeazor, ta ce fiye da mata da kananan yara 90,000 ne ke mutuwa duk shekar a sanadiyar shakar hayakin itacen girki.