Gwamnatin Tarayya za ta rage farashin gas din girki
Ministan ya bayyana cewa Najeriya na da arzikin iskar gas, saboda haka ba za a bari lamarin ya ci gaba da kamari ba.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwarta kan tsadar farashin gas din girki wanda hakan ya sa ta kafa kwamitin da zai yi aiki don rage farashin nan da mako guda.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ekperikpe Ekpo ne ya yi tsokaci kan kalubalen da ke tattare da samar da man fetur da kuma farashin gas din girki.
- Abdullahi Abbas zai maka Dederi a kotu kan zargin APC da murɗe shari’ar Gwamnan Kano
- Tottenham ta yi rashin nasara wasa uku jere a Firimiyar Ingila
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan hauhawar farashin gas din girkin, wanda ake sayar da kilogiram daya kan Naira 950 zuwa Naira 1050 a wasu sassan kasar nan.
Aminiya ta ruwaito cewa farashin ya haura N1200 kan kowace kilogiram a jihohin Kano, Katsina da kuma Kaduna.
Ekpo, a cikin wata sanarwar, ya ce manyan kalubalen da aka gano da suka sa farashin gas din ya tashi na da alaka da karancin gas din da ake shigowa da shi a baya-bayan nan.
Ministan ya bayyana cewa Najeriya na da arzikin iskar gas, wanda ya ce ba gwamnati ba za ta bari lamarin ya ci gaba da kamari ba.
A dalilin haka ne ministan ya kafa wani kwamiti karkashin jagorancin shugaban Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur ta Najeriya (NMDPRA) kan yadda za a bunkasa kayayyaki da kuma karya farashin gas din girki cikin mako guda.