Gwamnatin Tarayya za ta sake fasalin Filin Wasa na MKO Abiola da ke Abuja
Gwamnatin ta amince da gina ƙananan cibiyoyin wasanni 20 a sassan ƙasar domin haɓaka wasanni a matakin ƙasa.
Gwamnatin Tarayya ta ɗaura aniyar ƙaddamar da sabon aiki na sake fasalin Filin Wasa na Moshood Abiola da ke Abuja domin inganta harkokin wasanni a ƙasar.
Aikin, wanda Hukumar Wasanni ta Ƙasa za ta jagoranta, zai haɗa da sake yi wa babban filin wasan sabuwar shimfiɗa da titin guje-guje, tare da gyara ɗakunan ‘yan wasa, cibiyar yaɗa labarai, ɗakunan manyan baƙi, tsarin tsaro da na sanarwa, da kuma rufin filin wasan.
- ’Yan sanda sun kashe ’yan bindiga sun ƙwato bama-bamai a Zamfara
- Wajibi ne jadawalin INEC ya yi daidai da tanadin Dokar Zaɓe — Kotu
Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Malam Shehu Dikko, ya ce matakin na daga cikin shirin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na amfani da wasanni wajen bunƙasa matasa da tattalin arziki.
Shirin zai kuma haɗa da kafa cibiyar horas da ‘yan wasa ta zamani, gyaran masaukin ‘yan wasa, wurin iyo, sabbin filayen atisaye, da sanya fitilu da na’urorin taya alƙalancin wasa na VAR masu inganci da tafiya da zamani.
Haka kuma gwamnatin ta amince da gina ƙananan cibiyoyin wasanni 20 a sassan ƙasar domin haɓaka wasanni a matakin ƙasa.