Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa iyalai dubu 40 da abinci a Adamawa

A ranar Laraba, 20 ga Satumba ce, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta fara rarraba abinci da nufin tallafa wa iyalai sama da dubu 40 abinci mai gina jiki a kananan hukumomi bakwai da aka ceto daga Boko Haram a Jihar Adamawa. kaddamar da shirin, ya gudana ne a karkashin Shugaban Hukumar […]

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa iyalai dubu 40 da abinci a Adamawa

A ranar Laraba, 20 ga Satumba ce, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) ta fara rarraba abinci da nufin tallafa wa iyalai sama da dubu 40 abinci mai gina jiki a kananan hukumomi bakwai da aka ceto daga Boko Haram a Jihar Adamawa. kaddamar da shirin, ya gudana ne a karkashin Shugaban Hukumar NEMA, Alhaji Mustapha Maihaja, wanda ya samu wakilcin Mista Slaku Luggard, shugaban shirin rarraba kayan abinci na Gwamnatin Tarayya a Adamawa a garin Gombi.  A cewar Hukumar NEMA, tirelolin abinci 206 ne za a raba a matsayin agaji ga kananan hukumomin Gombi da Hong da Maiha da Mubi ta Kudu da Mubi ta Arewa da Michika da Madagali. Kayayyakin sun hada da waken suya da gero da garin masara da samobita da masabita ga iylan gidajen na tsawon wata daya. An tsara shirin ne bayan an zabo wadanda suka cancanci su ci gajiyar shirin a yankunan bakwai.

Da yake mayar da jawabi a madadin wadanda za su ci gajiyar shirin, Hakimin Gombi, Alhaji Shu’aibu Barde ya gode wa Gwamnatin Tarayya kan wannan tallafi.