Lalube kawai Gwamnatin Tinubu take yi —Atiku
Dokar, “ta fito da dabi’ar Gwamnatin Tinubu, kamar matukin jirin ruwan da ya bace a tsakiyar teku,” in ji Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce yanayin Gwamantin Tinubu daidai yake da mota a tsakiyar jeji babu direba.
Atiku ya bayyana gwamtin a matsayin mara alkibla ce a yayin da yake sukan sabon tsarin da ta bullo da shi na haramta wa dalibai yan kasa da shekaru 18 zana jarabawar kammaa sakandare.
Dokar, “ta fito fili da dabi’ar Gwamnatin Tinubu, wadda take daidai da matukin jirin ruwan da ya bace a tsakiyar teku,” in ji shi.
A martanin da ya wallafa ranar Laraba a shafinsa na X, Atiku ya ce dokar ba komai ba ce face kassara harkar neman ilimi.
- Rabon Gado: Alkali ya soke hukuncin kotun Musulunci
- ’Yan Najeriya miliyan 31.8 na fuskantar ƙarancin abinci — Rahoto
Ana iya tuna cewa Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya riga ya sanar da cewa babu gudu babu ja da baya kan maganar shekaru 18 a matsayin mafi karancin shekaru ga dalibai masu zana jarabawar shiga manyan makarantu.
Amma tsohon dan takararn shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023 din ya bayyana dokar a matsayin koma-baya ga harkar ilimi, domin kuwa dokar tane neman hana yancin neman ilim.
A don haka ya ce ya kamata kowa ya fito ya yi tir da ita, inda ya ci gaba da cewa, “Tsarin mulkin Najeriya ya sanya ilimi a jerin ayyukan yau da kullum wadda gwamnatocin jihohi ke da karfin iko a kai fiye da ta Tarayya.
“Saboda haka dokar ilimi da Gwamnatin Tarayya ta yi daidai yake da mulkin kama-karya.
“Abin da aka sani a kasaseh shi ne jihohi su yi irin wadannan dokoki a bangaren ilimi; abin haushin shi ne yadda gwamnatin ba ta yi wani tanadi domin dalibai masu basira ba, wanda hakan ke nuna ba ta san muhimmancinsu ba.“