‘Gwamnatin Tinubu na shirin dawo da farashin Dala N750 kafin Disamba’
Farashin canjin Dala na ci gaba da yin tashin gwauron zabi a baya-bayan nan a Najeriya.
Gwamnatin Tarayya ta ce tana wani yunkuri na rage farashin Dalar Amurka zuwa Naira 750 nan da watan Disamba.
Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Manufofin Kasafin Kudi da Sake Fasalin Haraji, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta Bloomberg.
- An shiga rudani bayan rushe fadar basarake a Abuja
- Miji ya nemi matarsa ta biya shi miliyan 1.5 kafin ya sake ta
Ya ce hakan zai hada da bullo da sabbin ka’idojin musayar kudaden kasashen waje, da suka hada da yaki da hada-hadar kudaden haram, domin rage gibin kashi 45 cikin 100 tsakanin farashin Dala da ake sayar da ita a yanzu haka.
Taiwo ya ce gwamnati za ta kuma kawar da koma-bayan bukatar dalar da aka yi kiyasin ta kau biliyan 6.7, za ta inganta kasuwancin Naira, da kuma kafa dokoki kan yadda ake gudanar da harkokin kasuwar.
“Har ila yau, akwai nufin fadada kasuwannin hukuma don hadawa da duk wata mu’amala ta halak, yayin da za a lalata haramtacciyar hanyar kasuwancin kudaden waje,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Muna tunanin duk wadannan za su faru ne kafin watan Disamba, kuma watakila nan da makonni biyu za mu fara ganin sakamakon, ta yadda kafin karshen shekara Naira za ta dawo ainihin darajarta.”
Shugaban ya kuma ce “farashin gaskiya” na dala bai wuce Naira 650 zuwa 750 ba, ko kuma 802.59, amma farashin N1,165 na kasuwar bayan fage ne.
A baya-bayan nan dai, ’yan kasuwa sun koka kan yadda farashin canjin Dala ya kara tashi, lamarin da ya kara haifar da tashin kayan masarufi.
An dai jima ana dambarwa game da batun farashin canjin kudaden waje a Najeriya.