Gwamnatin Tinubu za ta binciki yadda Buhari ya tafiyar da shirin N-Power
Gwamnatin ta kuma ce ta dakatar da shirin gaba daya
Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin N-Power har sai abin da hali ya yi.
Ministar Jinkai da Yaki da Talauci, Betta Edu ce ta sanar da daukar matakin a cikin tattaunawarta da gidan talabijin na TVC a ranar Asabar.
- Rikicin Isra’ila da Hamas: An kashe Falasdinawa 198, Yahudawa 40
- ‘Babu wata jami’a a Najeriya da ta kai ABU Zariya samar da kwararru a fannin shari’a’
Ta ce sun yanke shawarar daukar matakin ne sakamakon gano wasu kura-kurai da suka yi a cikinsa.
Ministar ta kuma ce tuni gwamnatinsu ta kaddamar da bincike kan yadda aka kashe kudade a cikin shirin tun a lokacin da aka kirkire shi.
Ta kuma ce yanzu haka, akwai wasu daga cikin wadanda ke cin gajiyar shirin, amma sam ba sa zuwa wuraren ayyukansu.
Betta Edu ta ce wasu daga cikin irin wadannan mutanen ya kamata a ce sun fita daga cikin shirin tun a shekara ta 2022, amma har yanzu ana ci gaba da biyansu albashi.
Ta ce, “Akwai abubuwa da dama da suke tafiya ba daidai ba. Akwai lokutan da muke tuntubar makarantun da suke aiki, amma ba sa nan. Ba sa aiki amma suna ikirarin suna bin mu bashin albashin wata takwas ko tara.
“Kusan kaso 80 cikin 100 na wadannan mutanen ba sa aiki amma suna neman hakkokinsu,” in ji Ministar.
Idan za a iya tunawa, tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya kirkiro shirin na N-Power a shekara ta 2016 da nufin rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa, kuma ake biyan masu amfani da shi N30,000 a kowanne wata.