Gwamnatin Yobe mai zuwa ta matasa ce – Dokta Goje

Shugaban Matasan Shiyyar A na Jam’iyyar APC a Jihar Yobe kuma Shugaban Kungiyar Matasan Masu Yakin Sake Zabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jJhar Dokta Muhammad Goje ya ce gwamnatin matasa za a yi a Jihar Yobe a wannan karo. Dokta Goje ya bayyana haka ne a lokacin da yake zanta wa da Aminiya a […]

Gwamnatin Yobe mai zuwa ta matasa ce – Dokta Goje

Dokta Muhammad Goje

Shugaban Matasan Shiyyar A na Jam’iyyar APC a Jihar Yobe kuma Shugaban Kungiyar Matasan Masu Yakin Sake Zabar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jJhar Dokta Muhammad Goje ya ce gwamnatin matasa za a yi a Jihar Yobe a wannan karo. Dokta Goje ya bayyana haka ne a lokacin da yake zanta wa da Aminiya a garin Damaturu, inda ya ce a tarihin siyasar Jihar Yobe ba a taba siyasa irin wannan lokaci ba inda aka zabi Gwamna matashi, mai kishi wanda zai dora daga inda maigidansa Ibrahim Gaidam ya tsaya.

Ya ce Gwamna Ibrahim Gaidam ya bunkasa harkar ilimi da lafiya da kuma bunkasa harkokin ci gaban matasa a Jihar Yobe ta hanyar daukar nauyin karatun dubban matasa a kasashen waje da cikin gida, sannan zababben Gwamnan, Alhaji Mai Mala Buni ya yi niyar dorawa.

Ya ce tun lokacin yakin neman zabe, zababben Gwamna Mai Mala Buni, yake cewa idan ya ci zabe matasa ne suka ci zabe domin da su za a yi wannan gwamnati.

Dokta Goje, ya ce gogewar da Mai Mala Buni ke da ita a harkar rayuwa da sanin mutane a duniya ba Najeriya kadai ba, da ita zai yi amfani wajen ganin an kawo wa Jihar Yobe abubuwan ci gaba na raya kasa.

A cewarsa zababben Gwamnan ya yi alkawarin kara habaka harkokin kasuwanci da ci gaba da tallafa wa ’yan kasuwar Jihar Yobe wajen kara wa masu karamin jari tallafi don ci gaba da kuma rage zaman kashe wando a tsakanin jama’a.

Sai ya yi kira ga  al’ummar Jihar Yobe su bai wa zababen Gwamnan hadin kai da goyon baya don sai ya samu hadin kai ne sannan duk wadannan abubuwan da ya yi niyya za su yiwu.