Gwamnatin Yobe ta jingine dokar hana talla a baro
Sakamakon matsin lamba daga al’ummar Damaturu, gwamnatin Jihar Yobe ta jingine dokar da ta kafa a makon jiya ta haramta amfani da baro wajen talla da kuma umarnin masu shagunan wucin-gadi da ke gefen titunan garin Damaturu su kawar da su. Da yake karin haske dangane da dakatar da amfani da dokar, Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli […]
Sakamakon matsin lamba daga al’ummar Damaturu, gwamnatin Jihar Yobe ta jingine dokar da ta kafa a makon jiya ta haramta amfani da baro wajen talla da kuma umarnin masu shagunan wucin-gadi da ke gefen titunan garin Damaturu su kawar da su. Da yake karin haske dangane da dakatar da amfani da dokar, Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli na Jihar Yobe Alhaji Idi Barde Gubana ya ce dakatar da amfani da dokar ya zama wajibi ganin cewar dokar za ta taba hakkokin jama’a, don haka an jingine amfani da dokar har sai lokacin da gwamnati ta tanada wa ’yan kasuwar da dokar za ta shafa matsuguni domin kada a shiga hakkinsu. Kwamishinan ya ce, an jingine dokar ce ba an yi watsi da ita ba, a’a sai nan gaba ne za ta fara aiki da zarar hukumar ta yi abin da ya kamata na tanadar wa da wadanda abin ya shafi matsuguni kamar yadda ya ambata a baya. Da Aminiya ta tuntubi wani jigo a kungiyar ’yan kasuwar kayan gwari Malam Bala Mai Tumatir wanda mambobinsu na daga cikin wadanda dokar za ta fi shafa ya ce hakika gwamnatin ta nuna dattaku da sanin ya kamata kan koke-koken da jama’a suka yi ta amince ta dakatar da amfani da dokar. Ya roki gwamnatin cewa in za ta samar musu da matsuguni ta samar musu matsugunin da jama’a za su iya bin su don sayen kayan ba matsugunin da ke nesa da jama’a ba.