Gwamnatin Yobe ta kara sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar

A sakamakon zaman da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya yi da sashin tsaro na jihar a ranar Talatar da ta gabata, gwamnatin jihar ta kara sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar da tun farko aka sa daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe. Yanzu an sabunta dokar ta koma daga […]

Gwamnatin Yobe ta kara sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni

A sakamakon zaman da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya yi da sashin tsaro na jihar a ranar Talatar da ta gabata, gwamnatin jihar ta kara sassauta dokar takaita zirga-zirga a jihar da tun farko aka sa daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe.

Yanzu an sabunta dokar ta koma daga karfe 11 na dare zuwa karfe 6 na safe, a duk fadin jihar ta Yobe. Bayanin hakan na dauke ne a wata takarda mai dauke da sanya hannun Babban Darakta mai kula da harkokin yada labarai na gwamnan jihar Abdullahi Bego.

Inda takardar ta kara tabbatar da cewa, gwamnati ta yi alkawarin ci gaba da aiki kafada da kafada da bangaren tsaron jihar don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.