Gwamnatin Zamfara ta dakatar da Hakimi saboda harin Karaye

Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle, ya amince da dakatar da babban Hakimin Gundumar Gummi Alhaji Abubakar Bala Gummi (Bunun Gummi). A wata sanarwa da Sakataren gudanawar masarautar Alhaji Aliyu Bello Maradun ya fitar, wanda ke cewa an dakatar da Hakimin ne nan ta ke sakamakon tuhumar da ake yi masa game da harin ’yan […]

Gwamnatin Zamfara ta dakatar da Hakimi saboda harin Karaye

Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle, ya amince da dakatar da babban Hakimin Gundumar Gummi Alhaji Abubakar Bala Gummi (Bunun Gummi).

A wata sanarwa da Sakataren gudanawar masarautar Alhaji Aliyu Bello Maradun ya fitar, wanda ke cewa an dakatar da Hakimin ne nan ta ke sakamakon tuhumar da ake yi masa game da harin ’yan bindiga a yankin.

Alhaji Aliyu, ya kara da cewa, “An dakatar da Alhaji Abubakar Bala Gummi, har zuwa lokacin da za a kammala binciken akan sanadiyyar kisan gillar da wasu ‘yan bindiga suka yi wa jama’ar kauyen Karaye kwanakin baya.”