Gwamnatina ba za ta lamunci sakaci da aiki ba – Tambuwal

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar ba-zata a Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Sakkwato da dare ranar Lahadin da ta gabata inda ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci sakaci da aiki ba. A lokacin ziyarar ya iske babu wutar lantarki a asibitin, lamarin da ya sa mafi yawan […]

Gwamnatina ba za ta lamunci sakaci da aiki ba – Tambuwal
Gwamnatina ba za ta lamunci sakaci da aiki ba – Tambuwal

Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kai ziyarar ba-zata a Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Sakkwato da dare ranar Lahadin da ta gabata inda ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci sakaci da aiki ba.

A lokacin ziyarar ya iske babu wutar lantarki a asibitin, lamarin da ya sa mafi yawan majinyata fitowa wajen daki suna kwanciya a kasa saboda tsananin zafi.
Fiye da minti 30 Gwamnan yana ziyarar asibitin kafin ma’aikatan da ke kula da janareton asibitin su fahimci Gwamna ne a asibitin su maido da wutar, kamar yadda kakakin Gwamnan Imam Imam ya fadi a wata sanarwa.
Ya ce Gwamnan ya yi addu’a ga majinyatan tare da yi musu alkawarin daukar matakin da ya dace kan harkokin lafiya a jihar.
Ya gargadi ma’aikatan da ke wasa da aikinsu, su tashi tsaye don ganin ba su sake aikata haka ba, saboda duk wanda aka samu na wargi da aikinsa zai fuskanci hukuncin da ya dace da shi.