Gwamnatinmu ba ta bukatar fadanci – Masari

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce, gwamnatinsa ba gwamnatin amshin Shata ba ce da za a ce mutum daya ke juya ta, gwamnati ce ta kowa ya kawo tasa gudunmawar domin ciyar da jiha gaba, kuma ba ta son fadanci a wajen gudanar da aiki. Gwamna Masari ya yi wadannan kalamai ne […]

Gwamnatinmu ba ta bukatar fadanci – Masari
Gwamnatinmu ba ta bukatar fadanci – Masari

Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya ce, gwamnatinsa ba gwamnatin amshin Shata ba ce da za a ce mutum daya ke juya ta, gwamnati ce ta kowa ya kawo tasa gudunmawar domin ciyar da jiha gaba, kuma ba ta son fadanci a wajen gudanar da aiki.
Gwamna Masari ya yi wadannan kalamai ne a wurin rantsar da karin masu ba shi shawara a dakin taro na Hukumar Kula da kananan Hukumomi da ke Katsina a ranar Talatar nan.
Gwamna Masari ya ce, ya rataya ga duk wanda yake da hakkin kawo wa jihar ci gaba ya bayar duk gudunmawar da zai iya bayarwa. “Ba mu ki a yi mana kalubale ga ayyukan da muke yi ba, amma idan za a yi suka mai amfani ba ta soki-burutsu ba. Saboda haka ya zama wajibi kuma babban aiki a wajenku na bayar da shawara tagari wadda za ta kawo ci gaban jihar nan,” inji Gwamnan.
Ya nanata kudirin gwamnatinsa na wajen ganin an samu ci gaba a fuskoki da dama, shi ya sa aka kirkiro ofishin mai bayar da shawara a fannin kwadago don ganin an sama wa jama’ar jihar abin yi.
Sababbin mashawartan da Gwamna Masari ya rantsar sun hada da Alhaji Rabi’u Idris Funtuwa Mai bayar da Shawara kan Dangantaka Tsakanin Gwamnati da Majalisar Dokoki da Alhaji Husaini Adamu Karaduwa Mai bayar da Shawara a kan Horarwa da daukar Ma’aikata da Alhaji Aminu Lawal (Maye) Jibiya, Mai bayar da Shawara kan kwadago da Ingancin Aiki.