Gwamnatocin baya ne suka jefa Najeriya cikin matsi — Onanuga
Onanuga ya ce gwamnatin Tinubu ba ta da laifin kan halin da ƙasar nan ke ciki a yanzu.
Fadar Shugaban Ƙasa ta ɗora alhakin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a kan gwamnatocin baya da suka shuɗe, inda ta ce gwamnatin Tinubu ba ta da laifi.
Mai bai wa shugaba Bola Tinubu na musamman, Bayo Onanuga ne, ya bayyana hakan, inda ya ce labarin da jaridar New York Times ta wallafa ya mayar da hankali ne kan abubuwa marasa kyau.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 6, sun sace wasu a Sakkwato
- HOTUNA: Yadda Sanusi II ya yi hawan sallah a Kano
A cewarsa kamata ya yi ta mayar da hankali kan haƙiƙanin halin da ake ciki da kuma ƙoƙarin da gwamnati mai ci ke yi na inganta tattalin arziƙi tun bayan hawa mulki a watan Mayun 2023.
Onanuga, ya jaddada cewar shugaba Tinubu ya gaji matsalolin tattalin arziƙi masu tarin yawa.
Ya ƙara da cewa, koma bayan tattalin arziƙi da suka haɗa da hauhawar farashin kayayyaki da basuka, ya samo asali ne daga tsare-tsare da aka daɗe ana yi kamar tsarin biyan tallafin man fetur da kuma karɓo basuka da gwamnatocin baya suka yi.
Onanuga, ya ce biyan tallafin man fetur da ake yi ya sa gwamnati rasa maƙudan kuɗaɗe tare da barin giɓin da zai ɗauki kafin a cike shi.
Don magance waɗannan ƙalubalen, gwamnati ta aiwatar da matakan samar da abinci da daƙile hauhawar farashin kayayyaki.
Wannan ya haɗa da saka hannun jari a harkar noma da bayar da tallafi ga manoma, da nufin rage tashin farashin kayan abinci da kuma ƙara wadatar da ƙasa da abinci.
Gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali kan gyara al’amuran tattalin arziƙi da aka gada ta hanyar sauye-sauyen manufofi daban-daban da za su kawo ci gaba mai tarin yawa ga Najeriya.