Gwamnoni 13 da Kotun Ƙoli ta tabbatar wa nasara

A Juma’ar makon jiya ce Kotun Ƙolin ta yanke hukunci kan zabukan gwamnonin jihohi bakwai.

Gwamnoni 13 da Kotun Ƙoli ta tabbatar wa nasara

Kotun Kolin Najeriya (Hoto: Onyekachukwi Obi)

A wannan Juma’ar ce Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukunci kan Zaɓen Gwamnan Jihar Nasarawa da wasu jihohi biyar.

Sauran jihohin da kotun ta yanke hukuncinsu a yau sun haɗar da Kaduna da Ogun da Kebbi da Gombe da kuma Jihar Delta, ta kuma jingine yanke hukunci kan Zaɓen Gwamnan Jihar Ribas.

Jihar Gombe

Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Inuwa Yahaya na Jam’iyyar APC a matsayin gwamnan jihar Gombe.

Kotun Ƙolin ta yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP, Jibrin Barde ya shigar na kalubalantar zaben gwamna Yahaya.

A hukuncin na bai ɗaya da kwamitin alkalai ya yanke, Kotun Ƙolin ta ce karar ba ta da inganci.

Jihar Kaduna

Kotun Ƙolin ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Isah Ashiru ya shigar yana kalubalantar nasarar Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna a zaben da aka gudanar na watan Maris ɗin bara.

Kotun Ƙolin ta kuma tabbatar da hukuncin da kananan kotuna suka yanke wato Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da kuma Kotun Daukaka Kara, wadanda suka tabbatar da nasarar Uba Sani a zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris na shekarar 2023.

Hukuncin dai ya kasance na bai ɗaya daga tawagar alkalan kotun kuma ba a ci tarar kowa ba.

Ana iya tuna cewa, gwamna Uba Sani ya sami kuri’u dubu 730 da 2, inda ya doke abokin hamayyarsa Mohammed Ashiru na jam’iyyar PDP mai kuri’u dubu 719 da 196.

Jihar Kebbi

Kotun Ƙolin ta kuma yi watsi da karar da Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya na jam’iyyar PDP ya shigar na kalubalantar nasarar zaben gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi.

A hukuncin da ta yanke a yau Juma’a, 19 ga watan shekarar 2024, tawagar alkalan kotun sun yi ittifaki kan cewa karar da dan takarar jam’iyyar PDP ya shigar ba ta da inganci.

Idan ana iya tunawa, Hukumar Zabe ta Kasa wato INEC, ta bayyana Nasir Idris a matsayin wanda ya lashe zaben na Jihar Kebbi da kuri’u dubu 409 da 225, inda ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya wanda ya sami kuri’u dubu 360 da 940.

An sami ratar kuri’u dubu 48 da 285 tsakanin gwamna Nasir Idris da abokin hamayyarsa Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya

Jihar Ogun

Kotun Ƙolin ta yi watsi da karar da Ladi Adebutu na jam’iyyar PDP ya shigar yana kalubalantar nasarar gwamna Dapo Abiodun na Jihar Ogun a yau Juma’a.

Karar kalubalantar nasarar Dapo Abiodun da Adebutu yi ta nuna cewa an saba wa Dokokin Zabe a zaben gwamna Abiodun kuma bai sami kuri’u mafi rinjaye ba don haka ya bukaci kotun ta soke zaben na ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

Sai dai a yau Juma’a, Kotun Ƙolin ta yi watsi da daukaka karar Adebutu a bisa rashin cancanta sannan ta tabbatar da nasarar Gwamna Abiodun a zaben na shekarar 2023.

Hukuncin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Kotun Ƙolin ta jingine yanke hukunci kan zaben gwamnan Jihar Ogun.

Ana iya tuna cewa, kotunan sauraron kararrakin zabe da na daukaka kara sun yi watsi da karar na dan takarar jam’iyyar PDP a baya.

Gwamna Dapo Abiodun ya sami nasara a zaben gwamnan Jihar Ogun ne da kuri’u dubu 276 da 298, inda ya doke abokan hamayyarsa da suka hada da Adebutu wanda ya sami kuri’u dubu 262 da 383 da kuma Biyi Otegbeye na jam’iyyar ADC wanda ya sami kuri’u dubu 94 da 754.

Jihar Delta

Hakazalika, a yau Juma’a ne Kotun Ƙolin ta yi watsi da kararraki uku na neman a soke zaben Sheriff Oborevwori a matsayin gwamnan Jihar Delta.

INEC dai ta bayyana Sheriff Oborevwori na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a Jihar Delta a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.

Sai dai saura ‘yan takarar uku bayan zaben ba su gamsu da sakamakon da hukumar INEC ta gabatar ba, inda suka garzaya zuwa kananan kotuna biyu.

A yayin da Oborevwori ya yi nasara a Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da kuma Kotun Daukaka Kara, bangarorin uku ba su gamsu ba, inda suka dauki matakin gaba na kalubalantar hukuncin kananan kotunan a Kotun Koli wanda ta zartar da hukuncinta a yau Juma’a 19 ga watan Janairun shekarar 2024 da muka shiga.

A lokacin da shari’ar ta Jihar Delta ta taso a kotun koli a yau, kotun ta amince da hukuncin da aka yanke a baya tare da tabbatar da nasarar Oborevwori a matsayin zababben gwamnan jihar Delta.

A yayin zartar da hukuncinta Kotun Kolin dai ta fara ne da yin watsi da karar sanata Ovie Omo-Agege na jam’iyyar APC da ya nemi a soke zaben Gwamna Oborevwori a bisa rashin iya tabbatar da zargin kada kuri’a fiye da kima da kuma rashin bin dokokin zabe ba.

A Juma’ar makon jiya ce, wato ranar 12 ga watan Janairu ne Kotun Ƙolin ta yanke hukunci kan zabukan gwamnonin jihohi bakwai da suka haɗa Kano da Bauchi da Zamfara da Ebonyi da Filato da Abiya da kuma Kuros Riba.

A duk hukunce-hukuncen da Kotun Ƙolin ta yanke na makon jiya, ta tabbatar wa da duk gwamnonin jihohin nasarar da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana musu bayan kammala zabe a watan Maris ɗin bara.

Cikin hukuncin da ya fi ɗaukar hankali, shi ne na Zaɓen Gwamnan Kano da Kotun Ƙolin ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen Gwamnan Kano bayan da Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da Kotun Daukaka Kara sun yanke hukuncin cewa kujerar gwamnan haramiyarsa ce.

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025