Gwamnoni ba su da ta cewa a kan tsaro – Gwamnan Jihar Zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’Aziz Yari ya ce gwamnoni ba su da ta cewa a kan sha’anin tsaro, kasancewar jami’an tsaro na karbar umarni daga Fadar Shugaban kasa ne.Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa ta musamman da ya yi da wakilanmu a Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara. Ya ce, idan da gwamnoni […]

Gwamnoni ba su da ta cewa a kan tsaro – Gwamnan Jihar Zamfara
Gwamnoni ba su da ta cewa a kan tsaro – Gwamnan Jihar Zamfara

Gwamna Alhaji Abdul’Aziz Yari na Jihar ZamfaraGwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’Aziz Yari ya ce gwamnoni ba su da ta cewa a kan sha’anin tsaro, kasancewar jami’an tsaro na karbar umarni daga Fadar Shugaban kasa ne.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ganawa ta musamman da ya yi da wakilanmu a Gusau, babban birnin jihar ta Zamfara.
Ya ce, idan da gwamnoni suna da ta cewa a jihohinsu, to ba za rika kai hare-hare hade da kashe mutane da kuma lalata dukiya da sace shanu ba tare da an kawo karshensu ba.
 Ya ce: “Idan har jami’an tsaro za su karbi umarni daga gwamnonin jihohinsu da tsaro bai tabarbare kamar haka ba. Daga Abuja ake ba jami’an tsaron da suke jihohi umarnin hani ko kuma yi. Abuja ta gwara kan gwamnoni da ’yan sanda da kuma sojojin da ke jihohi, idan aka zo batun yanke hukuncin yadda za a shawo kan matsalar tsaro, sai su ce sai sun samu umarni daga Abuja.”
A lokacin da Gwamnan yake yi wa wakilan Aminiya karin bayani game da kashe-kashen da ya ki ci ya ki cinyewa a Jihar Zamfara, wadanda suka janyo salwantar rayuka da kuma asarar dukiyoyi, sai ya ce, za a iya daukar mataki tun kafin a kai hare-haren, kasancewar gwamnati da jami’an tsaro sukan samu labarin za a kai harin, tun kafin a kai shi.
“Na ji takaici da bakin ciki sakamakon salwantar rayuka da kuma asarar dukiya da aka yi. Mun samu labarin za a kai kai harin, wanda hakan ya sanya muka yi bakin kokarinmu don mu dakile shi, bayan mun samu labarin ne sai muka sanya jami’an tsaro a wuraren da muke tsammanin za a kai harin, sannan muka sanya aka dakatar da ganawar da ’yan banga suke yi a jihar nan.
“Idan kuka yi la’akari, za ku ga ba wai an kai wa kauye hari ba ne, an kai wa ’yan bangar da ke tattaunawa a kan al’amarin tsaro ne. An kuma kai harin ne da misalin karfe 2:30 na rana. Maharan sun je kai tsaye ga ’yan bangar sannan suka rika kashe su.
“An san wadanda suke da hannu wajen kai harin, amma abin da akan tambaya shi ne, me gwamna ya yi a kan batun harin? (Ni a nawa bangaren) abin da zan iya shi ne ba da umarni wajen dakile shi, kuma na yi hakan. Abin da ya rage shi ne, wanda aka ba shi umarni, sai ya aiwatar da umarnin da aka ba shi.” Inji shi.
Ya ce matsalar tana wurin jami’an tsaro, “A kullum akwai matsala tsakanin ofishin Gwamnan Jiha da kuma jami’an tsaro. Akan ce gwamna shi ne Babban Jami’in Tsaro a jiharsa, amma ba zai iya fada wa kwamishinan ’yan sandan jiharsa cewa, ‘je wuri kaza ka kare rayuka da dukiyoyi’ ba, sai ya ce sai ya samu umarni daga Abuja.  Haka idan ka kira sojoji ka ce musu ‘mun samu labarin za a kai hari wuri kaza, ku je ku tsare tun kafin a kawo harin’, sai su ce sai sun samu umarnin hakan daga Abuja. Duk da haka kuma a rika kiran gwamna Babban Jami’in Tsaro? Anya hakan zai yiwu?”
Ya ce idan ta ra’ayinsa ne babu wani batun gwamna shi ne Babban Jami’in Tsaro jiharsa, saboda babu wani gwamna da yake da ta cewa a kan tsaro a jiharsa. “Idan ka yi musu magana sai su ce sun yi kadan, suna bukatar karin jami’an tsaro da sauran korafe-korafe. Ni ne gwamna, ni na san mutanena da kuma matsalolinsu, amma abin takaici, sai ka ji wani yana zaune a Abuja, kuma shi ne zai fada mini yadda zan shawo matsalar tsaro a jihata, kowa ya san idan aka tafi a haka ba za a samu nasara ba. Bai kamata a rika gudanar da mulki haka ba.” Inji shi.
Da aka tambaye shi ko ya taba rokon fadar Shugaban kasa a kan ta sakar masa mara don ya rika ba jami’an tsaro umarni kan al’amarin tsaro, sai ya ce: “Ba zan taba zuwa in roki wani don ya sake mini mara don gudanar da mulki jihata ba. Kodayake dukkan al’amarin da ya shafi tsaro na kasar nan yana karkashin Fadar Shugaban kasa ne, a matsayinmu na gwamnoni sai dai mu taimaka. Talaka da yake yawo a titi bai san cewa gwamna ba shi da ta cewa a kan tsaro a jiharsa ba. Jami’an tsaro kan zo wurinmu ne kawai idan suna da bukatar kudi ko abubuwan hawa lokacin da za su fita gudanar da aikinsu.  Don haka hakkin kare rayuka da kuma dukiyoyin al’umma ya rataya ne kacokam a wuyan shugaban kasa, shi ne Babban Kwamandan Askarawan Najeriya.” Inji Gwamnan na Jihar Zamfara.