Gwamnoni Bakwai na bata wa APC lokaci ne kawai
Daga Rilwanu Fajaldu Iyakar abin da na fahimta gwamnonin PDP bakwai da suke rigima ba za su fita daga Jam’iyyar PDP ba, su shiga Jam’iyyar PDM ko su kafa tasu sabuwa. In kuma ya zama lallai sai sun fita, mai yiwuwa sai nan gaba amma ba a kurkusa ba. Mutane suna tsammanin da shiga APC […]
Daga Rilwanu Fajaldu
Iyakar abin da na fahimta gwamnonin PDP bakwai da suke rigima ba za su fita daga Jam’iyyar PDP ba, su shiga Jam’iyyar PDM ko su kafa tasu sabuwa. In kuma ya zama lallai sai sun fita, mai yiwuwa sai nan gaba amma ba a kurkusa ba. Mutane suna tsammanin da shiga APC gwamnonin da fitarsu daga PDP kamar za a yi shi ne kiftawa da bisimilla. A ganina ba haka ba ne jan aiki ne sosai. Abubuwa hudu ne ko biyar in sun wuce su je shida na dogara da su a kan cewa duk wannan hayaniyar siyasa da takaddamar cikin gida ta ’yan bakwai, watan-watarana ba dadewa za a dawo a dinke, ba za a rabu ba.
Dalili na farko cikin shi ne: gwamnoni bakwai (shida daga cikinsu: Kano da Jigawa da Sakkwato da Neja da Adamawa da Kwara) a siyasa ba su da uwa da uban da ya wuce tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Kuma dukkansu suna matukar girmama tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida. Ba na tsammin wadannan mutane shida za su tsallake shawara ko umarnin wadannan mutum biyu. Duk sun san irin karfin da suke da shi na fada a ji da irin rawar da za su iya takawa in suka bi umarni ko suka saba. Da Obasanjo da Babangida ra’ayinsu shi ne G-7 su zauna a cikin PDP a yi duk rigimar da za a yi domin a kawo gyara a cikin gida. In har G-7 suka bijire suka shiga APC yanzu mai gidansu shi ne Bola Ahmed Tinubu wanda ba sa shiri da Obasanjo ko Buhari wanda ba sa shiri da Babangida. Ina ganin G-7 za su tsaya a bisa shawarwarin iyayensu na siyasa.
Dalili na biyu, shi ne duk gwamnonin nan bakwai da shugabannin APC suka ziyarta, babu wanda ya yi farat ya amshi wannan kokon bara. Abin da suka yi ittifaki a duk inda aka hadu da su shi ne, mu bakwai ne kuma ba mu kadai muke siyasa ba, za mu je mu yi shawara. A wurare uku ma da Jihar Ribas da Sakkkwato da Kwara, gwamnonin kamar cin fuskar zawarawansu suka yi. Domin shi Rotimi Ameachi cewa ya yi sai ya tuntubi Shugaban Goodluck Jonathan kafin ya dauki matsayi. Shi kuma Gwamnan Kwara cewa wannan sha’ani wuka da nama na hannun Sanata Bukola Saraki domin shi ya gaji siyasar mahaifinsa da ke juya a’almuran Kwara kusan shekara 40. Alliyu Magatakarda na Sakkwato cewa ya yi sam bai kulla wata yarjejeniya da kowa cewa zai shiga APC ba. Wannan matsayi ya nuna gwamnoni suna shawara, amma kowa ya san ba shawara suke yi ba, tunda jihohinsu su ne wuka da nama, a’a sun fi karkata a sulhunta a PDP su ci gaba da bin mashayarsu ta asali. Shi kuwa sulhu sai a hankali ake yi ba da gaggawa ba.
Dalili na uku, da nake zaton zai hana gwamnonin tsallakawa shi ne tsoro da fargabar abin da zai biyo baya. Duk cikinsu babu wanda ba ya da wani guntun kashi a gindinsa, wanda ana iya bankado shi a yi amfani da shi domin tozarta shi, ko suna gudun kada wata bukata da suke da ita wacce tana damfare da PDP su rasa ta in sun bar jam’iyyar. Idan da babu wani abu da suke hange da tuni sun yi adabo da PDP saboda ai suna son yin gwaninta da bin ra’ayin da jama’arsu ke kai, dama Shata ya ce matsoraci ba shi zama gwani kowane ne.
Dalili na hudu, shi ne ba duk masu wannan fadi tashi ne suke da matsaloli bai-daya ba. Wasunsu sun ari wannan rigima ne kawai suka yafa, ba wai domin ta shafe su kai-tsaye ba. Saboda haka idan aka tirza, aka ja daga, aka biyo ta bayan gida aka yi musu dauki dai-dai aka biya bukatunsu za su koma su yayyafa wa hayaniyar ruwa don ta lafa. Kuma in wadannan gwamnoni suka shigo APC ba lallai ba ne irin yadda suke watayawa a PDP a jihohinsu su samu. Za su je APC ne tare da tsintsinka musu mukamai, saboda a wurare da yawa ba za a bari su zama cinye duka ba, ka ga sun ci baya ke nan a wajen riko da madafun iko, kuma ko a wajen ba da wadanda za su yi takara. Amma in suka ci gaba da zama a jam’iyyarsu damar tana hannunsu sai yadda suka so. Ba za su so su rage wa kansu da kansu karfi ba.
Wani dalili da shi ma ina ganin zai hana su shiga APC shi ne saboda shakuwa da irin tsarin PDP. In suka shigo hadakar, dole za su rika hakuri da abubuwa yadda suka zo tunda gidan wani ne ba nasu ba. Bisa al’adar siyasarmu mai mulki zai rika tafiyar da komai nasa yadda ya saba, wannan kuwa zai jawo masa sabani da abokan da suka hadu. Za su gwammace su ci gaba da yin abin da suka saba maimakon canza salo.
Wasu da yawa cikin mutanen APC suna shaukin su ga ranar da wadannan gwamnoni za su shigo cikinta. A ra’ayinsu da fahimtarasu in sun taho APC hakan zai dada mata karfi, PDP za ta dada rauni, magoya baya za su karu, fatar Janar Buhari ya samu mulki ya dawo Arewa ya samu tagomashi, zaton Yarbawa sun samu tudun dafawa a Gwamnatin Tarayya zai tabbata. Idan ba su shigo ba, za su ji takaici. Kuma a cikin APC, akwai masu ra’ayin gwamnoni su yi zamansu can, saboda yadda suka fahimta in sun shigo an koma gidan jiya babu bambanci, an jawo wa kai rikici, an shafa wa APC bakin jinin da PDP ta dade da shi a wurin talakawa, sannan za a danne wasu domin a biya bukatar wasu. Idan ba su shigo ba ’yan wannan ajin za su zuba ruwa a kasa su sha.
Sakamakon wadannan dalilai, na fi karkata ga cewa bata wa APC lokaci wadannan gwamnoni ke yi, ba shigowa za su yi ba. Kawai APC ta ci gaba da aikin hada kan mutanenta a Arewa da Gabas da Kudu da Yamma domin fuskantar PDP. In sun taho daga bisani sai a karbe su da hannu bibiyu, in sun noke sai a yake su, a karbe jihohin nasu a gyara Najeriya.
Rilwanu Fajaldu
karamar Hukumar Dange/Shuni,
Jihar Sakkwato.
08066284826