‘Gwamnoni da dama ba za su iya biyan N70,000 mafi ƙarancin albashi ba’

Kuɗin da muke samu daga Gwamnatin Tarayya ba zai wadace mu biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba.

‘Gwamnoni da dama ba za su iya biyan N70,000 mafi ƙarancin albashi ba’

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa gwamnoni da dama ba za su iya biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 ba.

Gwamnan ya faɗi hakan ne yayin ganawa da wakilan ƙungiyoyin ƙwadago da fararen hula da ’yan kasuwa a Fadar Gwamnatin Gombe.

Gwamnan wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, ya nanata cewa kuɗin da suke samu daga Gwamnatin Tarayya ba zai wadace su biyan mafi ƙarancin albashin ma’aikata a jihohinsu ba.

A Litinin ɗin da ta gabata ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata.

Lamarin dai na zuwa ne a wani yunƙuri da Gwamnatin Tarayyar ta yi na ganin ta daƙile zanga-zangar matsin rayuwa da matasa ke shirin gudanarwa a faɗin ƙasar.

“Abu ne mai wahala na iya biyan N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi. Kuma ina tsammanin hakan take a sauran jihohi.

“Hatta tsohon mafi ƙarancin albashi na N30,000 da ƙyar wasu gwamnatocin jihohin ke biya ballatana a soma batun N70,000 ana fama da wannan matsin na tattalin arziki,” in ji gwamnan.

Gwamna Yahaya ya kuma bayyana cewa Jihar Gombe ta karɓi Naira biliyan biyu daga cikin Naira biliyan uku na tallafin rage raɗaɗi da Gwamnatin Tarayya ta bayar a bara.

Ya alaƙanta matsin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasar da cire tallafin man fetur da aka yi wanda a cewarsa ya samo asali ne tun daga gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Sai dai ya ce dole ce ta sanya Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur ɗin a ranar da yake karɓar rantsuwar kama ragamar aiki la’akari da cewa lissafin haka a cikin Kasafin Kuɗin Ƙasar na 2023.

Ya ƙara da cewa har kawo yanzu Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da biyan tallafin man fetur ɗin fiye da yadda take biya a baya.

A ƙarshe Gwamnan ya buƙaci duk masu ruwa da tsaki da su ɗauki wasu matakan a madadin zanga-zangar da ka iya rikiɗewa ta zama rikici.

’Yan sanda sun kama ’yan fashi 6 a Gombe

Mata sun yi zanga-zanga gabanin rantsar da Trump a Amurka

TikTok ya daina aiki a Amurka

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji