Gwamnoni da kuxin Kulob xin Paris kashi na biyu

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta sake wa jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya kimanin Naira biliyan 243 da miliyan 795 a matsayin kashi na biyu na kuxinsu da aka zabgtare da sunan biyan bashin kulob xin Paris. Wata sanarwar Ma’aikatar Kuxi ta Tarayya ta nuna jihohin Akwa Ibom da Bayelsa da Ribas da […]

Gwamnoni da kuxin Kulob xin Paris kashi na biyu

A makon jiya ne Gwamnatin Tarayya ta sake wa jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya kimanin Naira biliyan 243 da miliyan 795 a matsayin kashi na biyu na kuxinsu da aka zabgtare da sunan biyan bashin kulob xin Paris.

Wata sanarwar Ma’aikatar Kuxi ta Tarayya ta nuna jihohin Akwa Ibom da Bayelsa da Ribas da Delta da kuma Kano sun karbi kimanin Naira biliyan 10 kowacce, yayin da Legas da Katsina suka samu Naira biliyan 8 kowacce. Babban Birnin Tarayya ne ya samu kaso mafi karanta na Naira miliyan 684 da dubu 867.

Kason na biyu na tsuntsu daga sama gasasshe yana zuwa ne bayan wata bakwai da zuwan kaso na farko da aka biya jihohin a bara. Mayar wa jihohin kuxin ya biyo bayan zabtare musu kuxaxensu fiye da kima daga tushe don biyan bashin da ake bin su daga 1995 zuwa shekarar 2015. Idan za a tuna a shekarar 2005 gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo ta yi amfani da rarar kuxin man fetur aka samu sakamakon karuwar farashin man fetur a kasuwar duniya wajen biyan Kulob xin Paris da Kulob xin Landan bashin da suke bin kasar nan.

Daga baya jihohi da kananan hukumomi sun yi korafin cewa an zabtare musu kuxaxensu fiye da kima. Kuma duk da gwamnatin Obasanjo ta amince ta maido musu, gwamnatinsa da ta ’Yar’aduwa da ta Jonathan da suka biyo baya ba wadda ta mayar mudu da kuxaxen sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya zo. A bara ya amince ya maido wa jihohin kuxaxen bias wasu ka’idoji da suka haxa da yin amfani da wani kason kuxin wajen biyan ximbin bashin albashi da fansho da ake bin galibin jihohin. Kuma sakamakon raguwar kuxin shiga a Asusun Tarayya da karayar tattalin arziki, galibin jihohin sun gaza sauke nauyin da ke kansu na biyan albashi, kuma a wani matakin gaggawa, Buhari ya ba su tallafin gaggawa na tarayya a shekarar 2015 amma hakan bai warware matsalar ba.

Abin bakin ciki, kaso na farko na kuxin Kulob xin Faris da aka maida wa jihohin da ya kai Naira biliyan 516 da miliyan 380 shi ma ya gaza magance matsalolin albashi da fansho da ake bin jihohin. Wannan saboda bashin ya daxa yawa ne a wasu jihohin, sannan kuma gwamnoni da dama sun karkatar da kuxin wajen wasu abubuwa da suka haxa da biyan ’yan kwangila basussuka. Biyan ’yan kwangila ba laifi ba ne, sai dai wasu sun kama gudanar da manyan ayyuka da kuma wasu marasa muhimmanci.

A farkon watan Yuli, gwamnonin sun yi alkawarin cewa kashi na biyu na kuxin da za a mayar musu za a yi amfani da shi ne wajen biyan bashin albashi da fansho. kungiyar Gwamnoni ta Najeriya (NGF) ta faxi a wata sanarwa cewa a wani taro da shugabanta, Gwamnan Jihar Zamfara Abdul’Aziz Yari Abubakar ya jagoranta, gwamnonin sun amince su biya dukan basussukan albashi da alawus-alawus da ma’aikatansu suke bin su da zarar kashin na biyu na kuxin ya iso hannunsu. Ta ce: “Gwamnoni 36 a daren jiya sun amince za su biya basussukan albashi da fansho da ma’aikata ke bin su a kasar nan da zarar aka maido musu da kaso na gaba na kuxin Kulob xin Paris da Landan… Gwamnonin suna sane da korafe-korafe da kukan da ake yi kan rashin biyan basussukan albashi da fanshon da kuma kuncin da ma’aikacin Najeriya yake ciki.”

Sai dai ana sake musu kuxin a makon jiya, sai waxansu gwamnoni suka fara cewa kuxaxen ba za su iya biyan basussukan da ake bin jihohinsu ba, ko kuma za su kebe wani bangare ne na kuxin ga ma’aikatansu da sauran bayanai. Wannan kari ne a kan zarge-zargen cewa waxansu gwamnonin sun naxa “kwararr” waxanda ta hannunsu aka karkatar da wasu daga cikin kuxaxen kason farko kuma yanzu haka lamarin yana karkashin binciken hukumomin EFCC da ICPC.

Waxansu masu lura da al’amura sun ce faxuwar darajar Naira mafi muni a kan Dala ta faru ne a lokacin da aka ba da wancan kaso na farko, sakamakon yadda aka rika rige-rigen neman Dala da waxancan kuxaxe.

A wannann karo, muna kira ga gwamnonin su yi amfani da waxannan kuxaxe bisa adalci domin magance kuncin da ma’aikatansu da mutanensu suke ciki ta hanyar biyan dukan basussukan albashi da fansho. Wajibi ne su sadaukar da sauran kuxin wajen yin ayyuka masu amfani da za su magance matsalolin da suke addabar al’umma. Kuma muna kira ga kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) da sauran kungiyoyin fararen hula da na kare hakkin jama’a su mike tsaye domin tabbatar da an sarrafa waxannan kuxaxe yadda ya kamata.